Jirgin yakin NAF ya yi luguden wuta a wurin shagalin kasurgumin ɗan bindigan Katsina

Jirgin yakin NAF ya yi luguden wuta a wurin shagalin kasurgumin ɗan bindigan Katsina

  • Jirgin yaƙin rundunar sojin sama ya yi luguden wuta kan wurin shagalin bikin wani kasurgumin ɗan bindiga a Katsina
  • Bayanai sun bayyana cewa luguden wutan ya yi wa yan ta'adda mummunan ɓarna, ya tura manyan su barzahu
  • Wani mazuanin kauyen da abun ya faru ya ce daga cikin waɗan da aka kashe har da wani gawurtacce mai suna Sule

Katsina - Yan bindiga da dama sun mutu yayin da jirgin yaƙin rundunar sojin sama (NAF) ya saki ruwan bama-bamai a shagalin aure da aka shirya wa ɗaya daga cikin shugabannin yan bindiga a Katsina.

Leadership ta rahoto cewa daga cikin waɗan da harin ya tura barzahu har da wani mai suna Sule, wani sanannen jagoran yan bindiga, ɗan uwan makashi, Lalbi Ginshima.

Kara karanta wannan

Rikici: An kaure tsakanin sojoji da wasu matasa, an hallaka mutane akalla 6

Dakarun sojojin sun kaddamar da wannan farmakin ne a ƙauyen Unguwar Adam, ƙaramar hukumar Dan Musa a jihar Katsina.

Taswirar jahar Katsina
Jirgin yakin NAF ya yi luguden wuta a wurin shagalin kasurgumin ɗan bindigan Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wata Majiyar fasaha ta bayyana cewa dakarun sojin sun samu rahoton sirri na cewa an ga yan bindiga sun nufi Anguwar Adam daga kauyen Ɗan Alikima domin ɗaura auren ɗaya ɗaga cikin shugabannin su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani babban jami'in fasaha a rundunar soji ya shaida wa PRNigeria cewa:

"Bisa wannan bayanai, Sojojin sama suka tashi jirgin sama domin sa ido kan lamarin a yankin da kuma tabbatarwa."
"Bayan wani ɗan lokaci jirgin ya tabbatar da sahihancin labarin saboda ganin yan bindiga sama da 50 na shagalinsu a wurin."

A cewar jami'in, Jirgin ya cigaba da bibiyar lamarin kuma ya tura wa jirgin yaƙi adireshin wurin da yan ta'addan suka koma a arewacin Anguwar Adam.

Kara karanta wannan

Binciken Mako: Kayan Masarufi uku da suka yi tashin gwaurin zabi a babbar kasuwar Najeriya

Ya ce:

"Jirgin yaƙin na isa wurin ya gano akwai sama da yan bindiga 50, ba da ɓata lokaci ba ya fara harba musu rokoki, igwa da sauran makamai."

Shin mutanen yankin sun san abin da ya auku?

Wata majiya a ƙauyen ta bayyana cewa yan ta'addan sun yi babban rashi, domin da yawan su sun bakunci lahira, wasu da dama sun ji munanan raunuka.

"An yi wa yan ta'addan mummunar ɓarna, aƙalla 27 daga cikin su sun tafi gana wa da Allah, yayin da wasu da yawa suka ji muggan raunuka."
"Daga cikin waɗan da aka sheke har da shugaban yan bindiga Sule, ɗan uwa ga ƙasurgumin ɗan bindiga, Lalbi Ginshima."

A wani labarin.na daban kuma Yan bindiga sun bindige Hadimin gwamna har Lahira a wurin ta'aziyya

Wasu tsagerun yan bindiga sun tare hadimin gwamnan Taraba , Honorabul Gbashi, sun bindige shi har Lahira.

Wani wanda ke tare da mamacin ya bayyana cewa sun baro wurin Jana'izar da suka halarta yayin da maharan suka tare su.

Kara karanta wannan

Jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya tsaya tsakiyar daji saboda mai ya kare

Asali: Legit.ng

Online view pixel