2023: Sanata Aisha Binani za ta nemi takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC

2023: Sanata Aisha Binani za ta nemi takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC

  • Sanata Aishatu Dahiru Ahmed ta bayyana shirinta na neman kujerar gwamna a jihar Adamawa
  • Binani mai wakiltar Adamawa ta tsakiya a majalisar dattawa ta ayyana burinta a sakatariyar APC
  • Shugaban APC na jiha ya yi alkawari cewa jam’iyya za ta ba masu neman takara dama su gwabza

Adamawa - Sanata Aishatu Dahiru Ahmed wanda aka fi sani da Binani, ta bayyana shirinta na neman takarar kujerar gwamna a zabe mai zuwa.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 16 ga watan Maris 2022, inda aka ji Aishatu Dahiru Ahmed tana harin kujerar gwamnar jihar Adamawa.

Sanata Aishatu Ahmed ta sanar da Duniya hakan ne a ranar Talata a lokacin da ta ziyarci sakatariyar jam’iyyar APC a birnin Yola, jihar Adamawa.

Sanatar ta Adamawa ta tsakiya ta yi wa ‘ya ‘yan jam’iyyar hamayyar alkawari cewa idan ta lashe zaben gwamna a 2023, za ta kawo sauyi a Adamawa.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Ban Taɓa Shan Kaye a Zaɓe Ba Tunda Na Shiga Siyasa Kimanin Shekaru 50 Da Suka Shuɗe, Adamu

Aishatu Dahiru Ahmed ta koka a game da halin da jihar Adamawa ta ke ciki duk da irin arzikin ta.

Sanata Aisha Binani
Sanata Aishatu Dahiru Ahmed Hoto: aisha_binani
Asali: Twitter

Adamawa ta na baya - Binani

“Duk da tarin albarkar al’umma da na arzikin kasa da Ubangiji ya yi wa jiharmu, mu ne na 25 a cikin jihohi 36 a alkaluman inganta rayuwar al’umma.”

- Aisha Dahiru Ahmed

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Sanata Dahiru Ahmed ta ce za tayi aiki dare da rana wajen ganin abubuwa sun sake zani idan tayi nasarar zama gwamna.

Jawabin shugaban APC

Shugaban jam’iyyar APC na reshen jihar Adamawa, Alhaji Ibrahim Bilal ya tabbatarwa ‘yan majalisar cewa za a ba kowa damar neman takara a zabe.

Jaridar ta rahoto Alhaji Bilal yana cewa APC ta shirya karbe mulkin jihar Adamawa a shekarar badi.

Kara karanta wannan

2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu

A zaben 2019 ne mulki ya bar hannun jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan inda Ahmadu Fintiri na PDP ya doke gwamna mai-ci, Sanata Jibrila Bindow.

Siyasar Adamawa

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Sanata Binani za ta yi takara da irinsu Elisha Abbo wanda abokin aikinta ne a majalisa wajen neman tikitin jam’iyyar APC.

Binani mai shekara 50 a Duniya ta taba wakiltar Yola/Girei a majalisar wakilan tarayya. A wancan lokaci 'yar siyasar tana tare da jam'iyyar PDP ne.

Wanene magajin Mai Rusau?

A makon nan ne mu ka kawo maku rahoto cewa har an fara tseren wanda zai gaji kujerar Nasir El-Rufai a karkashin jam’iyyar APC a jihar Kaduna a 2023.

Akwai wasu mutane 11 zuwa 14 da ake tunanin daga cikinsu ne za a samu sabon gwamna a Mayun 2023. Daga cikinsu akwai Uba Sani da Sani Dattijo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel