Daga Karshe, Gwamna El-Rufa'i ya faɗi yankin da Magajin Shugaba Buhari zai fito a 2023

Daga Karshe, Gwamna El-Rufa'i ya faɗi yankin da Magajin Shugaba Buhari zai fito a 2023

  • Gwamnan Kaduna, Malam El-Rufai ya ce APC na tsammanin ɗan takarar da zata tsayar ya fito daga kudancin kasar nan
  • Gwamnan ya ce duba da kai kujerar shugaban jam'iyya arewa, suna tsammanin ɗan kudu ne zai gaji shugaba Buhari a 2023
  • El-Rufai ya kuma zare kansa da maganar neman takara, amma ya ce idan Buhari ya nemi ya yi, to ba zai ƙi ba

Abuja - Ana tsammanin ɗan takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023 dake tafe ƙarƙashin jam'iyyar APC zai fito ne daga yankin kudancin Najeriya.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ne ya yi wannan furucin ranar Laraba, yayin wata fira da Channels Tv.

Gwamnan ya yi bayanin cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa zai fito daga Arewacin Najeriya, dan haka suke tsammanin magajin Buhari ya fito daga kudu.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai
Daga Karshe, Gwamna El-Rufa'i ya faɗi yankin da Magajin Shugaba Buhari zai fito a 2023 Hoto: The Governor Of Kaduna State/facebook
Asali: Facebook

A kalamansa, El-Ruafa'i ya ce:

"Muna tsammanin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023 zai fito ne daga wani wuri a yankin kudancin Najeriya."

A cewar Malam Nasiru, ƙusoshin jam'iyyar APC a kudu ne zasu zauna su ga wane ɓangare daga yankinsu za su baiwa takarar.

Tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja ya ƙara da cewa, "Wuka da nama na hannun jiga-jigan APC na kudu su zakulo mana nagartaccen ɗan takara da za'a amince da shi."

Shin APC zata iya kai bantenta a 2023?

Gwamna El-Rufa'i ya nuna kwarin guiwarsa da cewa APC zata cigaba da rike kujera lamba ɗaya a Najeriya, inda ya yi ikirarin cewa jam'iyyar na da duk abin da ake bukata na cigaba da mulki.

"Ina da yakinin a zaben 2023, APC zata lashe zaben shugaban ƙasa da kuma adadi mai yawa na kujerun gwamnoni."

Gwamnan ya kuma zare kansa wajen shiga takarar wata kujera a zaɓe mai zuwa, amma yace zai iya fitowa takara matukar shugaba Buhari ya umarce shi da yin haka.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta mika kujerar shugabanta na ƙasa yankin Arewa ta tsakiya

Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan, ta fitar da jadawalin rarraba ofisoshin shugabanninta zuwa yanki-yanki yayin da ranar babban gangamin taro na kasa ke kara matsowa.

A jadawalin da APC ta fitar yau Laraba a Abuja, jam'iyyar ta miƙa ofishin shugaban jam'iyya na ƙasa zuwa yankin arewa ta tsakiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel