Kwadayin 2023, Jonathan, FFK da abubuwa 5 da suka jawowa Buni matsala a tafiyar APC

Kwadayin 2023, Jonathan, FFK da abubuwa 5 da suka jawowa Buni matsala a tafiyar APC

  • Wasu gwamnonin APC sun yi nasara wajen sauke Mai Mala Buni daga shugabancin jam’iyya na kasa
  • Ana zargin gwamnan na jihar Yobe da aikata wasu laifuffuka da-dama, daga ciki akwai kin shirya zabe
  • A karshe tsohon sakataren na APC ya rasa kujerarsa kamar yadda ta faru da Oyegun da Oshiomhole

A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta kawo dalilai da ake zargin sun taimakawa Mai Mala Buni wajen rasa jagorancin APC na rikon kwarya da yake yi tun 2020.

1. Kin shirya zabe

Babban zunubin da ake tuhumar Mai Mala Buni da aikatawa shi ne ya ki shirya zaben shugabannin jam’iyya na kasa, kwamitinsa ya yi ta daga lokacin zabe.

A matsayinsa na shugaban rikon kwarya da gudanar da zabe, ya kamata a ce Buni ya rike jam’iyya ne na gajeren lokaci, sai a zabi cikakkun shugabanni na kasa.

Kara karanta wannan

Yadda Lauyoyin Mala Buni suka shirya makarkashiya domin yakar APC inji El-Rufai

2. Neman jawowa APC matsala

Irinsu Gwamna Nasir El-Rufai su na ganin an yi amfani da Mai Mala Buni wajen yi wa APC barazana, har an kai ta kara domin a dakatar da shirya zaben shugabanni.

Gwamnonin na APC su na tunanin tun da kwamitin CECPC bai dauki wani mataki ba, ‘yan takarar APC za su iya rasa kujerunsu ko da sun samu nasara a zaben 2023.

3. Harin takara a 2023

Wasu su na da ra’ayin cewa abin da ya sa Gwamna Mala Buni ya yi ta jan lokaci tun Yunin 2020 har zuwa yanzu shi ne saboda harin takarar mataimakin shugaban kasa.

FFK a APC
Buni, Fani-Kayode a Aso Villa Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Rahotanni sun ce ana zargin Buni yana neman shugabancin kasa a karkashin APC, har ta kai yana tunanin sauka daga kujerar gwamnan idan zai zama shugaban APC.

Kara karanta wannan

Rikicin gida: Gwamnoni 6 da suka shiga suka fita, har suka ga bayan Mai Mala Buni a APC

4. Zawarcin Jonathan

Akwai masu zargin cewa Mala Buni da mutanensa ne suke kokarin jawo tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan cikin jam’iyyar APC da nufin a ba shi tikitin takara.

Sakataren rikon kwarya na jam’iyya na kasa watau Sanata John Akpanudoedehe ya taba nuna hakan, har ya bayyana cewa shigowar Jonathan za ta amfani APC kwarai.

5. Jawowa APC kowane tarkace

Mala Buni ya yi kokari wajen ganin wasu daga cikin gwamnonin adawa sun sauya-sheka zuwa APC. A haka ne jam'iyyar APC ta karbe Zamfara, Ebonyi da Kuros Riba.

Sai dai kuma bayan zargin zawarcin Jonathan, gwamna Buni ya shigo da irinsu Femi Fani-Kayode cikin APC, wanda hakan sam bai yi wa wasu ‘ya ‘yanta dadi ba.

An yi waje da shi - El-Rufai

Ku na da labari cewa Gwamna Nasir El-Rufai ya ce da an biyewa Mala Buni, watakila duka ‘yan takarar APC a 2023 za su iya rasa kujerunsu kamar yadda aka yi a Zamfara.

Kara karanta wannan

Sabon shugaban APC ya dauki matakin farko na dunkule jam’iyya kafin Buni ya dawo

El-Rufai ya ce boyayyan nukiliya aka shirya domin a ruguza zaben shugabanni, don haka suka yi bakin kokarinsu wajen ganin an yi waje da Buni tun da ya ki daukar mataki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel