Jerin manyan jihohi 5 a Najeriya da suka fi yawan rumfunan zabe

Jerin manyan jihohi 5 a Najeriya da suka fi yawan rumfunan zabe

Domin ganin an gudanar da babban zaben 2023 cikin lumana, gaskiya da amana, yan Najeriya da dama na ta kira ga hukumar zabe da kasa mai zaman kanta (INEC) da ta samar da Karin rumfunan zabe a fadin kasar.

Idan har INEC ta dauki wannan shawara, ko shakka babu, zai magance matsalar halin ko in kula na masu zabe sannan zai matso da tsarin zaben kusa da mutane.

A halin yanzu wasu jihohi sun yiwa sauran fintinkau ta fannin yawan adadin rumfunan zabe a kananan hukumomi.

Jerin manyan jihohi 5 a Najeriya da suka fi yawan rumfunan zabe
Jerin manyan jihohi 5 a Najeriya da suka fi yawan rumfunan zabe
Asali: Original

Wani bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa akwai jihohi biyar da mafi yawan sabbin rumfunan zabe a Najeriya.

A kasa akwai jerin jihohi biyar da adadin rumfunan zaben da suke da shi:

Kara karanta wannan

Sanatoci ga INEC: Ya kamata fursunoni a Najeriya su kada kuri'a a zaben 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Lagos: 4,861

2. Kano: 3,148

3. Kaduna: 2,910

4. Rivers: 2,424

5. Plateau: 2,358

Sanatoci ga INEC: Ya kamata fursunoni a Najeriya su kada kuri'a a zaben 2023

A wani labarin, majalisar Dattawa ta bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta bai wa fursunonin da suka cancanta damar kada kuri’a a duk zabukan kasar nan, rahoton Channels Tv.

Majalisar ta tattauna hakan ne a zamanta na ranar Talata a lokacin da ta yi nazari kan kudirin ba da dama ga fursunoni don kada kuri’a a babban zabe a Najeriya wanda Sanata Abba Moro ya dauki nauyi.

Sun yi kira ga INEC da ta tantance matsayin fursunonin da kundin tsarin mulki ya amince da rajistarsu a matsayin wadanda suka cancanci kada kuri’a kuma su kada kuri’a a lokacin zabe.

Kara karanta wannan

Shiga aikin soja: Abubuwa 5 kuke bukata domin shiga aikin sojin Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel