Buhari bai lamunce mun don darewa kujerar shugaban APC na kasa ba – Sanata Abdullahi Adamu

Buhari bai lamunce mun don darewa kujerar shugaban APC na kasa ba – Sanata Abdullahi Adamu

  • Sanata Abdullahi Adamu ya karyata rade-radin da ake yi na cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na goyon bayansa domin ya zama shugaban jam'iyyar APC na kasa
  • Maimakon haka, Adamu wanda ya bayyana hakan a wajen wani taron 'ya'yan jam'iyyar a Keffi, ya bukace su da su yi masa addu'an samun nasara a babban taro mai zuwa
  • Tun farko dai an tattaro cewa gwamnoni da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar basa goyon bayan tsayar da tsohon gwamnan na Nasarawa

Nasarawa - Tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma babban dan takarar kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana cewa sabanin abun da ke ta yawo a kafafen yada labarai, Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai tsayar da shi ba.

Kara karanta wannan

Bello ya zama Shugaban APC na rikon kwarya, Buhari ya yarda a tuntuke Mala Buni

Sanata Adamu ya yi karin hasken ne a Keffi yayin da ya karbi bakuncin jami’an jam’iyyar a matakin karamar hukuma a mahaifarsa ta Keffi, a ranar Asabar, Nigerian Tribune ta rahoto.

Idan za ku tuna, a yayin ganawar karshe da APC ta yi, an tattaro cewa shugaban kasar ya tsayar da Sanata Adamu kuma cewa hakan bai yiwa masu ruwa da tsaki da gwamnonin jam’iyyar dadi ba.

Buhari bai lamunce mun don darewa kujerar shugaban APC na kasa ba – Sanata Abdullahi Adamu
Sanata Abdullahi Adamu ya ce Buhari bai tsayar da shi ba Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Wasu gwamnoni sun bayyana cewa Sanata Adamu ba cikakken dan jam’iyya bane, inda suka ce ya kamata wanda ya san ciki da wajen jam’iyyar ne zai jagorance ta amma ba wai tsohon dan PDP ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnonin sun kuma yi zargin cewa rawar da ya taka a matsayin shugaban kwamitin sasanci na APC bai kai a bashi wannan kujera ba.

Ku yi mun addu'an samun nasara a babban taron jam'iyya - Sanata Adamu

Kara karanta wannan

Da ace EFCC na aikinta yadda ya kamata, da wasu masu neman kujerar Buhari suna kurkuku - Obasanjo

Sai dai kuma, wata majiya wacce ta halarci taron Keffi ta ce sanatan ya fadawa wadanda suka hallara cewa su yi watsi da rahoton cewa Buhari ya lamunce masa.

Ya fada masu da su yi addu’a domin nasararsa a babban taron jam’iyyar da za a yi a ranar 26 ga watan Maris, 2022.

Majiyar ta ce:

“Sanata Adamu ya fadama wadanda suka halarci taron cewa Shugaba Buhari bai lamuncewa kowani dan takara don darewa kujerar shugaban jam’iyyar na kasa ba.
“Maimakon haka, Sanata Adamu ya nemi jami’an jam’iyyar su yi addu’a don samun nasararsa a matsayin shugaban APC na kasa na gaba.”

A cewar majiyar, tsohon gwamnan ya roki jami’an jam’iyyar da su tara akalla mutane 100 daga kowani gudunmar zabe da za su yi mashi rakiya zuwa babban taron jam’iyyar da za a yi.

Shugaban APC na kasa: Magoya baya sun hada N10m don siyawa zabin Buhari fam

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Magoya baya sun hada N10m don siyawa zabin Buhari fam

A gefe guda, shugaban kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Nasarawa, Dr Kassim Muhammed Kassim, ya bayyana cewa sun tara naira miliyan 10 domin siyawa Sanata Abdullahi Adamu tikitin takara.

Kassim ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki daga yankin arewa ta tsakiya ne suka hada kudin, Daily Trust ta rahoto.

Tsohon gwamnan na jihar Nasarawa yana hararar kujerar shugaban APC na kasa a babban taron jam’iyyar mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel