Rudani: Rikicin shugabanci ya taso a NNPP yayin da Kwankwaso ke shirin shiga cikinta

Rudani: Rikicin shugabanci ya taso a NNPP yayin da Kwankwaso ke shirin shiga cikinta

  • Jim kadan bayan da Kwankwaso ya bayyana kudurinsa na shiga NNPP, jam'iyyar ta fara fuskantar rudanin shugabanci
  • Shugaban jam'iyyar ta NNPP a jihar Kano, Hisham Habib ya nuna adawa da sauyin shugabanci a jihohi na jam'iyyar
  • Ya ce sam bai kamata a manta da wadanda suka yiwa jam'iyya hidima ba, a kawo baki su rike mukamai a cikinta

Jihar Kano - Shugaban jam’iyyar NNPP a jihar Kano, Hisham Habib, ya nuna adawa da rushe shugabancin jam’iyyar na jiha da kwamitin zartaswar jam'iyyar ta yi, yana mai cewa matakin ya saba ka’idojin dimokradiyya.

Jam’iyyar NNPP ta kara samun karbuwa a yankin Arewa, kwanaki kadan bayan da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso ya bayyana shirinsa na shiga jam’iyyar.

Jam'iyyar NNPP na iya shiga damuwar shugabanci
Rudani: Rikicin shugabanci ya taso a NNPP yayin da Kwankwaso ke shirin shiga cikinta | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

A ranar Laraba, Habib ya ce jam’iyyar na maraba da shigowar Kwankwaso cikinta, amma ya sani cewa ba za a bashi tikitin tsayawa takara ba kai tsaye, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito a baya.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta kori dukkan shugabanninta yayinda Kwankwaso ke shirin sauya sheka jam'iyyar

Daily Nigerian ta tattaro cewa bayan rushe shugabancin jam'iyyar na jihohi a fadin kasar nan, jam’iyyar ta nada Umar Doguwa ya shugabanci Kano.

Doguwa dai tsohon shugaban jam’iyyar APC ne a Kano, kuma dan tsagin Kwankwaso, yanzu kuma NNPP ta nada shi a matsayin shugaban riko a jihar Kano.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Habib ya bayyana adawarsa, ya ce matakin a mamaya ce ta kungiyar Kwankwasiyya karkashin jagorancin Kwankwaso kan jam'iyyar NNPP.

Hakazalika, ya ce dole a duba cikin tsanaki, kana zai dauki matakan kotu kan wannan lamarin rushe shugabancin.

Ya kuma nuna damuwarsa cewa siyasar bangaranci na iya zama da hadari matukar ‘yan siyasa za su iya murde tafiyar da jam’iyyu daga wadanda suka dade suna mata hidima.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Jam’iyyar NNPP, Hashim Habib, Ya Yi Maraba Da Kwankwaso, Amma Ya Yi Masa Wani Muhimmin Gargaɗi

A cewarsa:

"Shugabancin jam'iyya na kasa na sane da kalubalen da muka fuskanta tsawon shekaru a yayin da muke tallata jam'iyyar, don haka mun cancanci samun kyakkyawar kulawa."

2023: Kwankwaso zai dawo jam’iyyar mu, NNPP ta bayar da tabbaci

A wani labarin, jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta ce suna kan tattaunawa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso akan batun komawar sa jam’iyyar kafin zuwan zaben 2023, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kamar yadda jam’iyyar ta shaida, nan da ‘yan kwanaki kadan tsohon gwamnan da tawagar sa za su koma jam’iyyar NNPP.

Dama tun a kwanakin baya aka samu bayanai akan yadda Kwankwaso yake shirin komawa wata jam’iyyar don tsayawa takarar shugaban kasa bayan ya soki APC da PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel