Jam'iyyar NNPP ta kori dukkan shugabanninta yayinda Kwankwaso ke shirin sauya sheka jam'iyyar

Jam'iyyar NNPP ta kori dukkan shugabanninta yayinda Kwankwaso ke shirin sauya sheka jam'iyyar

  • Jam'iyyar NNPP ta rusa kwamitin shugabanninta na jihohi da kasa ga baki daya
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa zata zabi wasu sabbi a taron gangamin da zata gudanar nan ba da dadewa ba
  • Kafin lokacin, an nada kwamitin rikon kwarya da zata gudanar da lamuran jam'iyyar na wata guda

Jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta rushe kwamitin shugabanninta na jiha da na tarayya gaba daya kuma ta nada sabuwar kwamitin rikon kwarya na wata guda.

Wannan ya biyo bayan jita-jitan dake yawo cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sauya sheka jam'iyyar.

Jam'iyyar ta ce zata zabi sabbin shugabanninta a taron gangamin da za'a gudanar, rahoton Leadership.

NNPP bata bayyana ranar taron gangamin ba.

La'alla rusa shugabannin jam'iyyar yana da alaka da sabbin mambobin dake shirin shiga.

Kara karanta wannan

Kafin karshen watan nan zan fita daga jam'iyyar PDP, Rabiu Musa Kwankwaso

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam'iyyar NNPP
Jam'iyyar NNPP ta kori dukkan shugabanninta yayinda Kwankwaso ke shirin sauya sheka jam'iyyar Hoto: NNPP
Asali: Twitter

Kafin karshen watan nan zan fita daga jam'iyyar PDP, Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa kafin karshen watan nan zai fice daga jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party PDP.

BBC Hausa ta ce tsohon gwamnan ya bayyana mata hakan.

Har ila yau Kwankwaso ya tabbatar da labarin cewa ya yi nisa a shirinsa na komawa jam'iyyar NNPP watau New Nigeria Peoples Party.

2023: Kwankwaso Zai Dawo Jam’iyyar Mu, NNPP Ta Bayar Da Tabbaci

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta ce suna kan tattaunawa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso akan batun komawar sa jam’iyyar kafin zuwan zaben 2023, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kamar yadda jam’iyyar ta shaida, nan da ‘yan kwanaki kadan tsohon gwamnan da tawagar sa za su koma jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Jam’iyyar NNPP, Hashim Habib, Ya Yi Maraba Da Kwankwaso, Amma Ya Yi Masa Wani Muhimmin Gargaɗi

Yayin tattaunawa da manema labarai, shugaban kwamitin zartarwa, NEC na NNPP, kuma sakataren jam’iyyar, Ambasada Agbo Major ya ce sun yi taro ne don tattaunawa akan yadda zasu bunkasa jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel