2023: Kwankwaso Zai Dawo Jam’iyyar Mu, NNPP Ta Bayar Da Tabbaci

2023: Kwankwaso Zai Dawo Jam’iyyar Mu, NNPP Ta Bayar Da Tabbaci

  • Jam’iyyar NNPP ta ce yanzu haka tana kan tattaunawa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso akan batun komawar sa jam’iyyar kafin zaben 2023
  • Jam’iyyar ta bayar da tabbaci inda ta ce nan da ba dadewa ba tsohon gwamnan zai koma jam’iyyar tare da duk wasu mutanen sa masu mara masa baya
  • Idan ba a manta ba, an samu jita-jita kan cewa Kwankwaso yana shirin komawa wata jam’iyyar ta daban don yakin neman shugaban kasar Najeriya

Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta ce suna kan tattaunawa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso akan batun komawar sa jam’iyyar kafin zuwan zaben 2023, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kamar yadda jam’iyyar ta shaida, nan da ‘yan kwanaki kadan tsohon gwamnan da tawagar sa za su koma jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da kakakin PDP ya rasu awanni bayan shagalin cika shekaru 50

2023: Kwankwaso Zai Dawo Jam’iyyar Mu, NNPP Ta Bayar Da Tabbaci
2023: Jam’iyyar NNPP Ta Bayar Da Tabbaci Kwankwaso Zai Shigo jam'iyyar ta. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Twitter

Dama tun a kwanakin baya aka samu bayanai akan yadda Kwankwaso yake shirin komawa wata jam’iyyar don tsayawa takarar shugaban kasa bayan ya soki APC da PDP.

Suna kan tattaunawa da Kwankwaso

Yayin tattaunawa da manema labarai, shugaban kwamitin zartarwa, NEC na NNPP, kuma sakataren jam’iyyar, Ambasada Agbo Major ya ce sun yi taro ne don tattaunawa akan yadda zasu bunkasa jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

Kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito, ya shaida cewa:

“Mu ‘yan NEC mun saba yin taro irin wannan, kuma muna yin shi lokaci bayan lokaci don tattaunawa akan matsaloli da kuma ci gaban jam’iyya, amma taron mu na yau na daban ne.
“Yanzu haka ‘yan Najeriya suna shirin babban zaben da ke karatowa kuma muna shirin gyara jam’iyyar sannan yanzu haka ‘yan Najeriya suna ta shiga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Duka Gwamnonin APC za su yi zaman musamman domin dinke sabuwar baraka kan mukamai

“Abinda zan iya shaida muku shi ne yanzu haka mun yi nisa a tattaunawar da muke yi da Kwankwaso kuma nan da ba dadewa ba zai dawo jam’iyyar NNPP tare da mabiyan sa.”

A cewarsa, jam’iyyar NNPP ba za ta yi maja da wata jam’iyyar ba

Ya ce jam’iyyar zata tsayar da Kwankwaso don ya yi takarar shugaban kasa inda yace babu wanda za a ba damar tsayawa takara in banda shi.

Ya kara da cewa Kwankwaso ya bukaci su janyo hankalin wasu ‘yan takarar don su tsaya a yi zaben fitar da gwani don mutane su fahimci muhimmanci ba jama’a damar zaben wanda suke so.

Sakataren ya kara da shaida cewa jam’iyyar ba za ta yarda ta yi maja da wata jam’iyya ba inda ya ce ta yi hakan a baya ba tare da ya haifar da wani ci gaba ba.

Ya shaida yadda suka hada kai da wasu jam’iyya a shekarar 2007 kuma basu ga wani ci gaba ba.

Kara karanta wannan

Gombe: Dan Majalisa Ya Fice Daga APC, Ya Ce Wasu Mambobin Za Su Bi Sahunsa

Ya ce babu wata jam’iyya ko kungiyar da suka hada kai da ita, a ko yaushe su suke yin abubuwan su da kan su.

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel