Kano: Shugaban Jam’iyyar NNPP, Hashim Habib, Ya Yi Maraba Da Kwankwaso, Amma Ya Yi Masa Wani Muhimmin Gargaɗi

Kano: Shugaban Jam’iyyar NNPP, Hashim Habib, Ya Yi Maraba Da Kwankwaso, Amma Ya Yi Masa Wani Muhimmin Gargaɗi

  • Hashim Habib, Shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, reshen Jihar Kano ya ce suna maraba da labarin shigowa Kwankwaso jam'iyyar
  • Sai dai Habib ya ce jam'iyyar ba za ta iya bada tabbacin cewa za ta bawa Kwankwaso tikiti kai tsaye ba sai dai ya yi takara a zaben cikin gida kamar yadda kundin tsarin mulkinsu ta tanada
  • Habib ya kuma mika godiyarsa ta musamman ga shugabannin jam'iyyar ta NNPP na shiyya da hedkwata na kasa bisa kokarinsu na tallata jam'iyyar a kasa

Kano - Shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ya nuna farin cikinsa kan sha'awar shiga jam'iyyarsu da mutane ke yi, yana mai cewa suna maraba da kowa amma ba bu tabbas cewa za su bawa wani tikitin takara kai tsaye.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Hashim Habib, Shugaban jam'iyyar a Kano, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ya ce jam'iyyar a shirye ta ke ta yi aiki tare da masu fatan shigowa jam'iyyar don cimma manufarsu, rahoton Daily Nigerian.

Kano: Shugaban Jam’iyyar NNPP, Hashim Habib, Ya Yi Maraba Da Kwankwaso, Amma Ya Yi Masa Wani Muhimmin Gargaɗi
Kano: Shugaban Jam’iyyar NNPP, Hashim Habib, Ya Yi Maraba Da Kwankwaso, Amma Ya Ce Ba Za a Bashi Tikiti Kai Tsaye Ba. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin Habib kan yiwuwar komawar Kwankwaso jam'iyyar

Da ya ke magana kan yiwuwar shigowar tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, cikin jam'iyyar, Mr Habib ya ce jam'iyyar ba za ta iya tabbatar da bada tikitin takara kai tsaye ga sabbin mambobin ba, sai dai su shiga zaben cikin gida kamar yadda kudin tsarin mulkin jam'iyya ta tanada.

Mr Habib ya ce:

"Muna fatan samun jihar Kano da Najeriya inda dukkan yan kasa za su samu damar iri daya."

Ya kara da cewa shugabannin jam'iyyar na kasa suna fatan hedkwatar jam'iyyar na kasa karkashin Dr Boniface Aniebonam za ta yi aiki don aiwatar da maja da hadin gwiwa tare da wadanda ke son shigowa jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Rikicin Masarautar Kano da Kamfanin jirgi: Ya kamata manya su saka baki, inji wata kungiya

Rahoton na Daily Nigerian ta ce Jam'iyyar a matakin jiha tana mika godiyarta ga shugabannin jam'iyyar a matakin shiyya da kasa bisa kokarinsu na tallata jam'iyyar.

Daily Nigerian ta rahoto cewa sakataren jam'iyyar NNPP na kasa mai barin gado, Agbo Gilbert Major, a ranar Talata, ya bayyana cewa Mr Kwankwaso na shirin shiga jam'iyyar.

2023: Kwankwaso Zai Dawo Jam’iyyar Mu, NNPP Ta Bayar Da Tabbaci

Tunda farko, Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta ce suna kan tattaunawa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso akan batun komawar sa jam’iyyar kafin zuwan zaben 2023, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kamar yadda jam’iyyar ta shaida, nan da ‘yan kwanaki kadan tsohon gwamnan da tawagar sa za su koma jam’iyyar NNPP.

Dama tun a kwanakin baya aka samu bayanai akan yadda Kwankwaso yake shirin komawa wata jam’iyyar don tsayawa takarar shugaban kasa bayan ya soki APC da PDP.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Yan bindiga sun halaka babban jami'in Kwastam a garin Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel