Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

  • Muhammadu Buhari da hadimai da sauran mukarrabansa sun samu kansu a cikin tsaka mai wuya
  • Dalilin kuwa shi ne zuwan sabuwar dokar gyaran zabe wanda za ta tilastawa wasu yin murabus
  • Watakila Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu, Babatunde Fashola, da Chris Ngige duk su yi murabus

Jaridar Daily Trust ta ce masu rike da mukaman gwamnati za su sauka idan har Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kudirin zaben da aka kawo masa.

Daga cikin abin da kudirin ya kunsa shi ne duk mai neman kujerar siyasa a 2023, zai yi murabus.

A wannan rahoto, an kawo Ministoci da kuma shugabannin cibiyoyi, ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da ake tunanin dole su ajiye mukamansu.

Ana rade-radin cewa irinsu Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu, Babatunde Fashola, da Chris Ngige su na harin takarar shugaban kasa a karkashin APC a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Yan bindiga sun halaka babban jami'in Kwastam a garin Kaduna

Haka zalika akwai jita-jitar Hadi Sirika; Sunday Dare, Abubakar Malami da Isa Pantami za su nemi takarar gwamna a jihohin Katsina, Oyo, Kebbi da Gombe.

Ministoci a FEC
Ministoci da Buhari a taron FEC Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

1. Rotimi Amaechi

Rotimi Amaechi bai bayyana cewa yana da sha’awar takarar shugaban kasa ba. Amma magoya bayansa sun fara yi wa ‘Dan Amanan na Daura kamfe tun yanzu.

2. Chris Ngige

Rahoton ya ce Dr Chris Ngige ya yi alwashin bayyana niyyarsa na neman takarar shugaban kasa Afrilu. Idan zai yi takara, ya wajaba ya sauka daga kujerar Minista.

3. Ogbonnoya Onu

Shi ma Ministan kimiyya da fasaha na kasa, Ogbonnoya Onu yana cikin wadanda ake gani yana da burin takarar shugaban kasa, idan yana da niyya, zai yi murabus.

4. Babatunde Fashola

Akwai Babatunde Fashola a jerin wadanda ake ganin za su iya zama shugaban kasa. Idan tsohon gwamnan yana da wannan buri, zai sauka daga Ministan ayyuka.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Buhari ya tsaida wanda yake so ya zama sabon Shugaban Jam’iyyar APC

Sauran masu mukamai

Ragowar shugabannin gwamnati da ake rade-radin za su nemi takara a zaben 2023 sun hada da irinsu Godwin Emefiele da Dr. Bashir Jamoh (takarar gwamnan Kaduna).

Ku na da labari cewa akwai alamun da ke nuna cewa ana zuga Mista Godwin Emefiele ya tsaya takarar shugaban kasa. Manyan APC na cikin masu hannu a wannan shiri.

Ana ganin Shugaban kasa ya yarda da Emefiele, kuma ya yi na’am da tsare-tsaren da ya kawo a CBN. Shi dai gwamnan babban bankin bai fito ya ce zai nemi takara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel