Wike: Lokaci Ya Yi, Yanzu Siyasar 'Cika Wa Mutane Ciki Da Abinci' Zan Fara

Wike: Lokaci Ya Yi, Yanzu Siyasar 'Cika Wa Mutane Ciki Da Abinci' Zan Fara

  • Gwamna Nyesome Wike na Jihar Rivers ya bayyana cewa yanzu lokaci ya yi da zai mayar da hankali wurin siyasar 'cika wa mutane ciki da abinci' wato stomach infrastructure
  • Gwamna Wike ya ce ya kammala yi wa mutanen jiharsa manyan ayyukan cigaba da gine-gine don haka abin da ya rage yanzu sai mayar da hankali wurin walwalar da jin dadinsu
  • Wike ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata yayin kaddamar da gadan sama ta Oro-Abali a mahadar Kaduna kan babban titin Port Harcourt-Aba a Port Harcourt

Rivers - An shiga murna a Jihar Rivers a ranar Talata bayan Gwamna Nyesome Wike ya ce daga yanzu gwamnatinsa za ta mayar da hankali ne wurin walwalar al'umma da bada tallafi da aka fi sani da 'Stomach Infrastruture'.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Gwamnan ya ce duba da cewa ya shafe shekarun farkonsa yana ayyukan gine-gine da more rayuwa, yanzu zai mayar da hankalinsa kan siyasar 'cika wa mutane ciki da abinci', The Nation ta rahoto.

Wike: Na Shiya, Yanzu Siyasar ‘Cika Wa Mutane Ciki’ Da Abinci Zan Fara
Wike Ya Ce Yanzu Siyasar ‘Cika Wa Mutane Ciki’ Da Abinci Zai Fara. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Twitter

Wike ya ce ya kammala yi wa mutanen jiharsa ayyuka, yanzu lokaci ne na siyasar 'cika ciki da abinci'

Ya ce:

"Yanzu mun kammala dukkan abubuwan da muka yi wa mutanen Rivers alkawari, yanzu ne lokacin ya kamata mu fara siyasar stomach infrastruture.
"Abin da mutane da ba su fahimta bane; mutane suna tunanin tun farkon ka shiga gwamnati, ka fara raba wa mutane kudi. Na ce ba zan yi hakan ba.
"Sai na fara yi wa mutanen jiha ta aiki. Yanzu kam mun yi aiki, sauran lokacin da ya rage kuma na cika ciki da abinci ne."

Kara karanta wannan

Ango Abdullahi: Dalilin da yasa bana goyon bayan tsarin karba-karba tsakanin shiyyoyi

Wike ya yi wannan jawabin ne yayin kaddamar da gadan sama ta Oro-Abali a mahadar Kaduna kan babban titin Port Harcourt-Aba a Port Harcourt, rahoton Nigerian Tribune.

Ya ce babu wanda zai zargi gwamnatinsa da rashin yin ayyuka, inganta tsaro da wanzar da zaman lafiya tsakanin al'umma a jihar.

Gwamna Wike ya cigaba da cewa walwala da jin dadin mutane abu ne mai muhimmanci a siyasa saboda tallafi ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel