Kotu ta yanke hukunci kan tsige gwamnan PDP da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
- Kotu ta ce laifi ne wani ya shigar da karar Ofishin gwamna Kacokan da zargin aikata ɗanyen aiki ko wani laifi
- Bisa haka Kotun jihar Ebonyi, ta yi watsi da karar dake bukatar shige gwamna Dave Umahi daga kujerarsa kan sauya sheka zuwa APC
- Alkalin Kotun, Mai shari'a Henry Njoku, ya umarci wanda ya shigar da kara ya biya gwamna N500,000 bisa bata masa lokaci
Ebonyi - Babbar Kotun jiha dake zamanta a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, ta yi watsi da ƙarar dake kalubalntar sauya shekar gwamna Dave Umahi zuwa APC.
Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna Umahi ya lashe zaben a shekarar 2015 da 2019 karkashin PDP kuma ya sauya sheƙa zuwa APC a watan Nuwamba, 2020.
Wanda ya shigar da kara, Sanata Sunny Ogbuoji, shi ne ɗan takarar gwamna karkashin APC, kuma ya zo na biyu a zaɓen shekarar 2019.

Asali: UGC
Ogbuoji ya garzaya Kotu ne domin ta share masa tantamar cewa ko gwamna Umahi zai cigaba da zama kujerar gwamna bayan ya sauya sheƙa zuwa APC.
Ya kafa hujja da Dokokin kwansutushin na 1999 wanda aka yi wa garambawul domin a tafka mahawara a Kotun.
Wane hukunci Kotu ta yanke?
Amma Alkalin Kotun, Mai Shari'a Henry Njoku, yayin da yake yanke hukunci, ya ce mai gabatar da ƙara ya dogara ne kan batun da ya shafi cancantar shiga zaɓe.
Alkalin ya ƙara da cewa babu wata doka a Kwansutushin da ta yanke hukunci kan tsige gwamna ko Mataimaki daga mukaminsa saboda ya sauya sheka.
Guardian ta rahoto Mai Sharia Njoku ya ce:
"Duba da abin da kowane bangare ya gabatar, Kotu ta yanke cewa wanda ake kara (Gwamna Umahi) bai saɓa wa kowace dokar ƙasa ko ta zaɓe ba dan ya koma APC."
"Kotu ta kuma yanke cewa duba da sashi na 308, laifi ne wani ya maka Ofishin gwamna a Kotu, dan haka Kotu ta yi watsi da karar baki ɗaya."
"Haka nan kuma ta ci tarar dubu N500,000 da wanda ya shigar da ƙara zai ba wa wanda ake kara saboda ɓata masa lokaci."
A wani labarin kuma mun kawo muku cewa Yan bindiga sun bindige Hadimin gwamna har Lahira a wurin ta'aziyya
Wani wanda ke tare da mamacin ya bayyana cewa sun baro wurin Jana'izar da suka halarta yayin da maharan suka tare su.
A halin yanzun dakarun sojoji sun bazama cikin daji domin nemo gawar mutumin, bayan sun yi gaba da ita.

Kara karanta wannan
Magana ta kare: Buhari ya tsaida wanda yake so ya zama sabon Shugaban Jam’iyyar APC
Asali: Legit.ng