Alkali ya bada umarni hukumar EFCC ta karbe wani gidan tsohon Gwamnan APC a Abuja

Alkali ya bada umarni hukumar EFCC ta karbe wani gidan tsohon Gwamnan APC a Abuja

  • EFCC ta fara samun nasara a kan Rochas Anayo Okorocha, Alkali ya bukaci a karbe wani katafaren gidan da ya mallaka
  • An bada adireshin gidan da 1032 & 1033 Cadastral Zone AO3, Takum Close, Off Michika Street, Ahmadu Bello Way, Garki Abuja
  • Hukumar EFCC ta na zargin cewa da kudin gwamnatin Imo aka saye gidan, don haka kotu ta ce a karbe sai sun karkare shari’a

Abuja- babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja ta yanke hukunci cewa a raba Rochas Anayo Okorocha da wasu gidajensa da su ke birnin Abuja.

EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta tabbatar da wannan a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook dazu da yamma.

Kara karanta wannan

Okorocha ya bada shawarar yadda za a magance rikicin APC ko APC tayi asarar Biliyoyi

Mai magana da yawun bakin EFCC na kasa, Wilson Uwujaren ya bayyana cewa su na zargin da dukiyar haram Rochas Okorocha ya mallaki wannan gidan.

Kamar yadda hukumar ta bayyana, za a raba tsohon gwamnan na jihar Imo da wannan kadara ne har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar da ake yi da shi.

Gidan talabijin na Channels TV ta rahoto cewa Alkali Emeka Nwite ya zartar da wannan hukunci a zaman da ya yi a ranar Alhamis, 24 ga watan Fubrairu 2022.

Hujjojin lauyoyin EFCC

EFCC ta kafa hujja ne da sashe na 44 (2) na kundin tsarin mulki na 1999 da kuma dokar Advance Fee Fraud and Other Fraud Related Offences Act No. 14 2006.

Tsohon Gwamnan Imo
Rochas Anayo Okorocha Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Lauyoyin da suka kai Sanatan na Imo kara sun bukaci Mai shari’an ya karbe wadannan dukiya.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta amincewa NDLEA ta ci gaba da tsare Abba Kyari da abokan harkallarsa 6

A cewar EFCC, bincikenta ya nuna mata gwamnatin Imo ta taba aikawa kamfanin Abtisal Global Ltd and Archivisual Solution Ltd, companies wasu N222m.

Ana zargin Rochas Okorocha ne ya mallaki wannan kamfanin wanda ta hannunsa aka saye gidan.

Hukuncin Alkali

A hukuncin da Emeka Nwite ya zartar, ya bukaci a karbe wannan gida da ke layin Ahmadu Bello Way a unguwar Garki a birnin tarayya Abuja na wani lokaci.

Emeka Nwite ya umarci hukumar EFCC ta wallafa labarin karbe gidan a manyan gidajen jaridun kasar nan domin ankarar da wadanda za su yi sha’awar gidan.

Shawarar Okorocha ga APC

A jiya ne aka ji tsohon Gwamnan jihar Imo, Rochas Owelle Okorocha, ya gargadi APC, ya ce zaben shugabanni na kasa da za a yi, zai iya karewa a rikicin kotu

Sanatan ya ce kin daukar wannan shawara da ya kawo zai jawo APC ta samu N2bn daga saida fam din takara, amma bayan nan ta kashe N3bn wajen shari’a.

Kara karanta wannan

Sakamakon zirga-zirgar Buhari: Kasar Ingila ta narka Naira Biliyan 5 domin inganta wuta

Asali: Legit.ng

Online view pixel