Hawaye sun kwaranya yayin da kakakin PDP ya rasu awanni bayan shagalin cika shekaru 50

Hawaye sun kwaranya yayin da kakakin PDP ya rasu awanni bayan shagalin cika shekaru 50

  • Allah ya yiwa mai magana da yawun jam'iyyar PDP a jihar Kwara, Tunde Ashaolu, rasuwa
  • Ashaolu ya rasu da yammacin ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu a Abuja, sa’o’i 24 bayan bikin cikarsa shekaru 50 a duniya
  • Jam'iyyar APC mai mulki a jihar ta mika sakon ta'aziyyarta ga iyalan mamacin da jam'iyyar adawar

Kakakin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Kwara, Tunde Ashaolu, ya kwanta dama.

Ashaolu ya rasu ne a yammacin ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, sa’o’i 24 bayan ya yi bikin cikarsa shekaru 50 a duniya, jaridar The Nation ta rahoto.

An tattaro cewa marigayin dan siyasar ya rasu ne sakamakon ciwon zuciya a babbar birnin tarayya, Abuja.

Hawaye sun kwaranya yayin da kakakin PDP ya rasu awanni bayan shagalin cika shekaru 50
Hawaye sun kwaranya yayin da kakakin PDP ya rasu awanni bayan shagalin cika shekaru 50 Hoto: Livenews.ng
Asali: UGC

An rahoto cewa tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya karbi bakuncin Ashaolu da tsohon shugaban karamar hukumar Ekiti na jihar, don liyafar zagayowar ranar haihuwarsa a Abuja.

Kara karanta wannan

Dan takarar PDP ya lashe zaben cike gurbi na Jos ta arewa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

APC ta mika sakon ta'aziyyarta

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar ta mika ta’aziyya ga babbar jam’iyyar adawar, rahoton Nigerian Tribune.

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar APC, Tajudeen Folaranmi ya fitar, ya amince da cewa marigayin ya sadaukar da kansa ga aikin kishin kasa na zurfafa tattaunawar siyasa a jihar.

Sanarwar ta ce:

“Muna kuma mika ta’aziyya ga iyalan marigayin wanda ya mutu ya bari.
"Muna addu'an Allah ya baiwa 'yan PDP da dangin marigayin hakurin jure wannan babban rashi da karfin zuciyar daukar wannan lamari."

Ma'aikacin Jami'ar Najeriya ya rasu yana tsaka da shakatawa a Swimming Pool

A wani labarin, mun kawo cewa wani ma'aikacin jami'ar Kalaba (UNICAL), Mista Ubong, wanda ke aiki a Ofishin Rijistara ya rasa rayuwarsa a ɗan karamin kwatamin ruwa a Kalaba, babban birnin jahar Cross Riba.

Kara karanta wannan

Gombe: Dan Majalisa Ya Fice Daga APC, Ya Ce Wasu Mambobin Za Su Bi Sahunsa

Jaridar Tribune ta rahoto cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na dare a Orange Resort swimming pool dake Lamba 151 kan hanyar MCC, cikin Birnin Kalaba.

Mutane sun tsinci gawar ma'aikacin jami'ar ne bayan ya fita domin shan iska kasancewar yanayin da ake ciki na zafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel