Da Duminsa: Shugaba Buhari Ya Baro Brussels Domin Koma Wa Aso Rock

Da Duminsa: Shugaba Buhari Ya Baro Brussels Domin Koma Wa Aso Rock

Shugaba Muhammadu Buhari yana hanyarsa na koma wa gida Najeriya bayan tafiyarsa zuwa Belgium inda ya hallarci taron hadin kai na EU-AU karo na shida.

Buhari Sallau, daya daga cikin hadiman Shugaba Muhammadu Buhari ne ya sanar da labarin tafiyarsa a shafinsa na Facebook.

Da Duminsa: Shugaba Buhari Ya Baro Brussels Domin Koma Wa Aso Rock
Shugaba Buhari Ya Baro Brussels Domin Dawo Wa Gida Najeriya. Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Sallau, a cikin rubutun da ya wallafa a ranar 19 ga watan Fabrairu ya ce:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya baro filin tashin jirage na Abelag/Luxaviation a Brussels domin koma wa Abuja bayan taron hadin kan African Union da European Union karo na 6 a Brussels, Belgium."

Asali: Legit.ng

Online view pixel