Siyasar Najeriya: Mata ta zata nemi takara a babban zaɓen 2023, Gwamna

Siyasar Najeriya: Mata ta zata nemi takara a babban zaɓen 2023, Gwamna

  • Gwamnan jihar Anambra dake gab da sauka kan mulki bayan karewar wa'adinsa, ya ce ba zai nemi wata kujerar siyasa ba a 2023
  • Gwamna Obiano ya ce mai dakinsa ce zata nemi takarar Sanata mai wakiltar mazaɓar Anambra ta arewa saboda yar can yankin ce
  • A ranar 17 ga watan Maris, 2022, wa'adin mulkin Obiano zai kare, kuma Farfesa Solido ne zai gaje sa bayan nasara a zaɓe

Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Chief Willie Obiano, ya tabbatar da cewa mai ɗakinsa, Ebele chukwu Obiano, zata nemi takarar Sanata a mazaɓar Anambra ta arewa a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa gwamnan ya yi bayanin cewa ba zai nemi wata kujera ba a zaɓen, zai koma gida ya huta bayan kammala mulki.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Rikici ya barke a mahaifar shugaba Buhari Daura kan wanda za'a ba takara a APC

Wa'adin mulkin gwamna Obiano na jihar Anambra zai ƙare ne a ranar 17 ga watan Maris, na wannan shekarar da muke ciki 2022.

Gwamna Obiano da mai ɗakinsa
Siyasar Najeriya: Mata ta zata nemi takara a babban zaɓen 2023, Gwamna Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kuma wanda zai gaje shi, shi ne tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Farfesa Chukwuma Soludo, wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake amsa tambayoyin yan jarida a mahaifarsa Aguleri, karamar hukumar Anambra East bayan duba wasu ayyukan da gwamnatinsa ta yi, gwamnan yace da zaran ya miƙa mulki, yana son hutawa bayan shafe shekaru 8.

Punch ta ruwaito Gwamna Obiano ya ce:

"Zan huta bayan wa'adin mulki na ya ƙare a jihar Anambra. Bana bukatar sai an faɗa mun na yi aiki ga mutanen jihata, saboda nasan na yi aiki tukuru."
"Wasu lokutan bani da kara a kan wannan, saboda nasan na hana ido na bacci domin tabbatar da na yi ayyuka sosai ga al'ummar jihar Anambra."

Kara karanta wannan

2023: Matashin ɗan takara dake son gaje kujerar Buhari ya shiga jihar Neja, ya nemi albarkar IBB

"Mai ɗakina ce ke son zuwa majalisar dattawa, tana son zata nemi takarar Sanata mai wakiltar Anambra ta arewa. Ita yar asalin ƙaramar hukumar Oyi ce a yankin Anambra ta arewa."

Mun maida filin jirgin mu na ƙasa da kasa - Obiano

Gwamna Obiano ya kara da cewa nan da mako biyu jirgin ƙasa da kasa na kamfanin Ethiopian Airlines zai sauka a filin jirgin Cargo and Passenger domin tabbatar da matsayinsa na kasa da ƙasa.

"Hakan zai kara habaka noma da kiyo, domin mutane za su samu damar fitar da kayayyakin su zuwa kasashen duniya cikin sauki."

A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar APC mai mulki ta ɗage gangamin taron ƙasa, ta sa ranar taron shiyyoyi

Jam'iyya mai mulkin kasar nan APC ta sanar da ranar da zata gudanar da zaɓen shugabanninta na shiyyoyin Najeriya.

APC ta ɗage babban taron ƙasa, amma ba ta sanar da sabuwar rana ba a wata wasika da ta sake aike wa hukumar zaɓe INEC.

Kara karanta wannan

Ku taimaka mun na gaji kujerar shugaba Buhari a 2023, Gwamna ya roki mambobin APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel