2023: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Salisu Tanko, Ya Goyi Bayan Shugabanci Ya Koma Kudu

2023: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Salisu Tanko, Ya Goyi Bayan Shugabanci Ya Koma Kudu

  • Shugaban jam’iyyar NCP na kasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar yayin zaben 2019, Yunusa Salisu Tanko ya bayyana goyon bayansa akan kudu ta amshi mulki a 2023
  • Ya yi wannan furucin ne yayin da manema labarai suka tattauna da shi a ofishin jam’iyyar, inda yace akwai bukatar a yi adalci da kuma daidaito tsakanin yankunan Najeriya
  • Tanko ya ce ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba, amma a cewarsa ya kamata a samar da shugaban kasa mai sa kaunar juna tsakanin yankunan bayan wannan gwamnatin ta kare, in har ana son ci gaban kasar nan

Abuja - Shugaban jam’iyyar NCP kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 na jam’iyyar, Yunusa Salisu Tanko ya bayyana goyon bayan sa akan shugabancin dan kudu, inda yace ya kamata a samu magajin Shugaba Muhammadu Buhari a 2023 daga yankin, The Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Magantu Game Da Batun Karɓa-Karɓa a Mulkin Najeriya

Tanko ya yi wannan maganar ne yayin tattaunawa da manema labarai a ofishin jam’iyyar a Abuja inda yace akwai bukatar yin adalcin a tsakanin ‘yan Najeriya.

2023: Shugaban Jam'iyyar NCP, Salisu Tanko, Ya Goyi Bayan Shugabanci Ya Koma Kudu
2023: Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa, Salisu Tanko, Ya Goyi Bayan Shugabanci Ya Koma Kudu. Hoto: The Sun
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda ya ce a wata takarda mai taken, “Siyasa hatsari ce”, dan siyasan ya ce:

“Wajibi ne mu samu shugaban kasa mai kishin kasa kuma wanda ko wanne yankin kasar nan zai amince da shi.”

Tanko ya ce ba zai tsaya takara ba

Tanko ya ce ba zai tsaya takara ba a 2023, amma ya ce yanzu haka kasa a rarrabe take don haka ya kamata a samo mai hada ta wuri guda, wanda ba zai nuna bambanci ba.

A cewarsa kamar yadda The Sun ta ruwaito:

“Kasar nan tana bukatar shugaban da zai sanya kaunar juna tsakanin jama’a, ya kuma sa wa kowa jin cewa shi dan kasa ne ko daga wanne yankin yake don samar da ci gaba."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jonathan Ya Goyi Bayan Gwamnan PDP Ya Zama Shugaban Ƙasa a 2023

Shugaban NCO ya bukaci Buhari ya sanya hannu akan dokokin zabe, inda yace matsawar bai yi hakan ba za a iya yin juyin mulki.

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel