2023: Magoya bayan Atiku sun buƙaci ya haƙura da takara, ya goyi bayan ɗan takara daga kudu

2023: Magoya bayan Atiku sun buƙaci ya haƙura da takara, ya goyi bayan ɗan takara daga kudu

  • Kungiyoyin magoya bayan Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya sun yi kira gare shi ya hakura da takarar shugaban kasa a 2023
  • Femi Osabinu, shugaban South-West Development Frontiers, a madadin sauran kungiyoyin ya ce shekaru sun fara wa Atiku yawa don haka ya hakura ya goyi bayan dan takara daga kudu
  • Kungiyoyin sun kuma bayyana cewa Najeriya tana bukatar shugaba ne mai karancin shekaru da kuzari da zai iya jure kallubalen da ke tattare da ofishin shugaban kasa

Gamayyar kungiyoyin masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun shawarci Turakin na Adamawa ya hakura da yin takarar shugaban kasa a 2023 amma ya goyi bayan dan takara daga kudu maso gabashin kasar.

Kungiyoyin sun hada da Middle Belt Network for Atiku, North For North Support Group for Atiku, Turaki Arewa Vanguard for Atiku da South-West Development Frontiers, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu gagarumin goyon baya daga wata kungiyar Inyamurai

2023: Magoya bayan Atiku sun bukaci ya hakura da takara, ya goyi bayan dan takara daga kudu
2023: Magoya bayan Atiku sun ce kada ya yi takara, ya goyi bayan dan takara daga kudu. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

Kawo yanzu Atiku bai sanar da zai yi takara ba a hukumance

Atiku bai riga ya bayyana cewa zai fito takarar shugaban kasar ba a hukumance amma ana hasashen yana shirin sake neman kujerar shugaban kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin da ya yi yayin taron manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, Femi Osabinu, shugaban South-West Development Frontiers, ya ce shekaru sun fara yi wa tsohon shugaban kasar yawa.

The Cable ta ruwaito cewa Osabinu ya ce Najeriya na bukatar matasahi mai jini a jika da zai iya jure ayyukan da ake bukata shugaban kasa ya yi.

Wani sashi cikin jawabinsa:

"Muna kira ga tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ya sake shawara game da niyyarsa na sake yin takarar shugaban kasa a 2023.
"Duk da cewa mun san Atiku ya hidimtawa kasa sosai, hakan yasa muka goyi bayansa tsawon shekaru, amma kuma bai dace mai shekaru 77 ya shiga takarar ba duba da irin kallubalen da kasar ke fama da shi.

Kara karanta wannan

Kotu ta aike ɗan gani-kashenin Atiku Abubakar gidan yari kan zagin Lamiɗon Adamawa

"Najeriya na bukatar matashi mai ji da karfi wanda zai hada kan kasa ya kuma iya jure wa yawan ayyukan da ke tattare da zama shugaban kasa ya kuma samar da mafita ga matsalolin Najeriya."

Ya kara da cewa mambobinsu a sassan kasar nan a wasu jam'iyyun suna tuntubar wadanda suka dace domin ganin an zabi shugaban kasa dan kudu a 2023.

Wadanda suka kira taron sun yi wannan kirar ga Atiku ne bisa la'akari da halin da kasar ke ciki a yanzu.

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel