Innalillahi: Sarkin Jama'are, Dakta Ahmadu Muhammad Wabi ya riga mu gidan gaskiya

Innalillahi: Sarkin Jama'are, Dakta Ahmadu Muhammad Wabi ya riga mu gidan gaskiya

  • Allah ya yi wa sarkin Jama'are, Alhaji Dakta Ahmadu Muhammad Wabi III rasuwa da karfe 12 na daren Asabar
  • Babban basaraken da ya kwashe shekaru hamsin kan karagar mulki ya rasu ya bar matan aure biyu, 'ya'ya 35 da jikoki da dama
  • Ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya kuma za a yi jana'izarsa da birne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar

Jama'are, Bauchi - Daga Allah mu ke, gare shi za mu koma. Ubangiji mai kowa mai komai ya dauka rayuwar Mai Martaba Sarkin Jama'are ta jihar Bauchi, Alhaji dakta Ahmadu Muhammad Wabi III.

Basaraken ya rasu wurin karfe 12 na daren Asabar wacce za ta sada mu da ranar Lahadi, shida ga watan Fabrairu kamar yadda Gado da Masun Jama'are, Alhaji saleh Malle ya sanar da BBC.

Kara karanta wannan

Harin Boko Haram a Buratai: Shugaban Sojoji ya ziyarci Borno, ya tattauna da Sojoji

Innalillahi: Sarkin Jama'are, Dakta Ahmadu Muhammad Wabi ya riga mu gidan gaskiya
Innalillahi: Sarkin Jama'are, Dakta Ahmadu Muhammad Wabi ya riga mu gidan gaskiya. Hoto daga bbc.com
Asali: UGC

Dakta Ahmadu Wabi ya koma ga mahaliccin sa ne bayan fama da rashin lafiyar da yayi.

Basaraken da ya shafe kimanin shekaru hamsin a kan karagar mulkin Jama'are, ya rasu ya bar matan aure biyu da 'ya'ya 35 da jikoki masu yawa.

Za a yi jana'izar sa tare da birne sa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a garin Jama'are.

Allah ya yi wa Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, rasuwa

A wani labari na daban, labari da duminsa da ke zuwa wa Legit.ng a yanzu shine rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.

Majiyoyi da dama da suke da kusanci da fadar sarkin sun tabbatar da rasuwarsa a yau Lahadi.

Marigayi Sarkin Zazzau shine Sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bindige tsohon dan takarar ciyaman da abokinsa

Majiyoyi da dama sun tabbatar wa Legit.ng cewa, basaraken ya rasu a asibitin 44 da ke Kaduna wurin karfe 11 na safiyar Lahadi.

"Tabbas Allah ya yi wa Sarki rasuwa. Ya kwanta rashin lafiya tun a ranar Juma'a kuma an kai shi asibiti inda ya rasu.
"Nan babu dadewa za a dawo da gawarsa Zaria domin fara shirin jana'izarsa," wata majiya mai kusanci da Iyan Zazzau ta tabbatar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel