2023: Dan Obasanjo ya yi alkawarin mara wa Osinbajo baya, Hadimin Buhari

2023: Dan Obasanjo ya yi alkawarin mara wa Osinbajo baya, Hadimin Buhari

  • Olojonwo, dan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bukaci a mara wa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo (SAN) baya a zaben shugaban kasa na 2023
  • Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman a harkar siyasa, Babafemi Ojudu ya sanar da hakan a wata wallafa da ya yi a Facebook ranar Asabar
  • A cewar Ojudu, Olujonwo ya kai masa ziyara ranar Juma’a inda ya bukaci ya basu goyon baya don mataimakin shugaban kasa ya nemi shugabancin Najeriya a 2023

Olujonwo, dan tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya nemi a goyi bayan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo (SAN) don ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023, The Punch ta ruwaito.

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman a harkar siyasa, Babafemi Ojudu ya sanar da hakan ta wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

2023: Kungiya ta bawa Osinbajo wa'adin kwanaki 30 ya fito ya nemi kujerar Buhari

2023: Dan Obasanjo ya kawo min ziyara, ya bukaci in mara wa Osinbajo baya, Ojudu
2023: Dan Obasanjo ya kawo min ziyara, ya bukaci in mara wa Osinbajo baya, Ojudu. Senator Babafemi Ojudu
Source: Facebook

A cewar Ojudu, Olojonwo ya je har wurin sa ranar Juma’a don ya nemi taimakon sa akan mataimakin shugaban kasa ya tsaya takara a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dama Ojudu ma’aikaci ne a ofishin mataimakin shugaban kasa

Ojudu wanda ya ke aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa ya wallafa:

“Olojonwo Obasanjo, dan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zo har wuri na jiya (Juma’a).
“Shi ma kamar saura ya zo don bayyana bukatar sa ta in mara wa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo baya don ya nemi kujerar shugaban kasa a 2023.
“Cikin dabaru ya yi alkawarin idan Osinbajo ya amsa kiran ‘yan Najeriya don ya tsaya takara, zai tsaya tsayin-daka don ci gaba da kamfen din neman kujerar.
“Mun gode Olu. Zan yada sakon ka.”

Dama Ojudu tun a baya ya ce ba zai goyi bayan Tinubu ba

Kara karanta wannan

Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze: Ba mu amince da shawarar Atiku ta yin wa'adi daya a mulkin Najeriya ba

The Punch ta ruwaito yadda Ojudu ya ce an dade ana tura maka sakonni daga fusatattu saboda ya ce ba zai goyi bayan takarar Bola Tinubu ba.

Ojudu ya ce ba zai goyi bayan Tinubu bane saboda dalilin da shi wanda ya bar wa kan sa sani kuma yana da damar yin hakan a siyasance.

A wata takarda da ya saki, Ojudu ya ce kin bin bayan tsohon gwamnan Jihar Legas ba alamar ya yi butulci bane.

Ya ce ba Tinubu bane ya mayar da duk wadanda suke alaka da shi mutum, dama da yawan su sun daukaka a lokacin da suka fara alaka da shi.

Dangane da kin bin Tinubu kuma ra’ayi ne, kowa da irin nasa. Ya ce ya wuce shekaru 60 da haihuwa kuma wurin neman hakkin siyasa har hannun jami’an tsaro ya shiga kuma ya fita.

Tinubu ne ya nemi Osinbajo ya tsaya a mataimakin shugaban kasa a zaben 2015

Osinbajo tsohon kwamishinan shari’a ne na Jihar Legas sannan Antoni Janar ne tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 lokacin Tinubu yana gwamna.

An samu rahoton yadda Tinubu ya zabi Osinbajo don ya tsaya a mataimakin shugaba Buhari lokacin zaben 2015.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon Shugaban Kwastam na Najeriya, Hamman Ahmad, ya rasu

A shekarar 2021 an ga Tinubu da Osinbajo a tare bayan dawowar Tinubu daga Amurka inda aka yi masa aiki a guiwar sa.

Duk da dai a ranar 10 ga watan Janairun 2022 Tinubu ya bayyana ra’ayin sa na tsayawa takara amma Osinbajo bai riga ya ce komai ba. Sai dai akwai masu mara masa baya da suke ta yi masa kamfen a wurare daban-daban a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164