Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze: Ba mu amince da shawarar Atiku ta yin wa'adi daya a mulkin Najeriya ba

Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze: Ba mu amince da shawarar Atiku ta yin wa'adi daya a mulkin Najeriya ba

  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo, ta yi watsi da rokon tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na yin shekaru 4 kacal idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023
  • Na hannun daman Atiku, Cif Raymond Dokpesi, ne ya yi wannan rokon a madadin ubangidan nasa
  • Sai dai Ohanaeze ta ce hakan bai samu karbuwa ba domin babu abun da zai hana yankin kudu maso gabas karbar mulki daga arewa a 2023

Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo, ta yi watsi da kudurin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na yin wa'adi daya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.

A cewar kungiyar, wannan shawara wata dabara ce da za ta hana yankin Kudu maso Gabas cimma manufofin siyasarta na farko na neman kujerar shugaban kasa.

Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze: Ba mu amince da shawarar Atiku ta yin wa'adi daya a mulkin Najeriya ba
Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze: Ba mu amince da shawarar Atiku ta yin wa'adi daya a mulkin Najeriya ba Hoto: Ndigbo Anambra chapter
Asali: Facebook

Ku tuna cewa Raymond Dokpesi, na hannun daman mai neman takarar shugaban kasar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar zai mulki Najeriya ne na tsawon shekaru hudu kawai idan har aka zabe shi a 2023, rahoton Punch.

Dokpesi ya sha alwashin yin zindir idan Atiku ya ki mika mulki ga Inyamurai bayan wa'adinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake martani, babban sakataren Ohanaeze, Okechukwu Isiguzoro, ya ce furucin cin mutunci ne ga mutanen kudu maso gabas, Sahara Reporters ta rahoto.

Isiguzoro ya kuma ayyana cewa Inyamurai ba za su karbi tikitin mataimakin shugaban kasa ba, inda ya ce yakamata a bari yankin ya samar da shugaban kasa a 2023.

A cikin sanarwar da ya sanyawa hannu, Isiguzoro ya tuna yadda Atiku ya yi watsi da bukatar yin shekaru hudu daga dattawan Igbo a 2019.

Ya ce:

“Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bayyana karara cewa yunkurin yaudarar yankin Kudu maso Gabas da kyawawan tayi da na hannun daman tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019, Raymond Dokpesi, ke yi don samawa ubangidansa Atiku goyon bayan kudu maso gabas a 2023 rashin mutunta hakkin jama’ar yankin ne, babu wani alkawari na jan hankali da zai sa Kudu maso Gabas su sayar da ‘yancinsu na shugabancin 2023 ga kowa.
"Rashin amincewa da tayin dattawan Igbo na yin wa'adi daya a 2019 da Atiku Abubakar bai yi ba zai ci gaba da kawo cikas ga kudirinsa na shugabancin kasar a 2023, maimakon haka, ya mayarwa shugabannin Igbo martani a 2019 da tsare-tsaren da shirya ma tattalin arzikin Najeriya na shekaru shida (2022-2026) wanda hakan ya nuna karara yana da kudirin yin wa'adi biyu idan aka zabe shi.
"Wannan hujjar ya saba da bukatar na hannun daman Atiku na neman goyon bayan kudu maso gabas, yayin da babu wata tawaga da za ta iya kawo shamaki ga shugabancin Igbo a 2023 da wannan bukata ta mataimakin shugaban kasar, wanda ba zai karbu ba, domin mulki zai bar arewa zuwa gabas a 2023."

Atiku shekaru 4 kadai zai yi idan ya hau mulki, Shugaban kwamitin yakin zabensa

A baya mun ji cewa Shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Cif Raymond Dokpesi, ya nemi yan Najeriya su zabi Atiku a 2023 saboda shekaru hudu kadai zai yi ya sauka.

Yace idan aka zabi Atiku kuma yayi shekaru hudu, yan yankin kudu maso gabas zasu samu daman gabatar da shugaban kasa a 2027.

Dokpesi ya bayyana hakan ranar Litinin a garin Umuahia, jihar Abia, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel