2023: Atiku ne zai iya kawo wa PDP nasara, Jigo a Jam'iyyar PDP

2023: Atiku ne zai iya kawo wa PDP nasara, Jigo a Jam'iyyar PDP

  • Wani jigo na jam’iyyar PDP a Jihar Edo, Barista Kenneth Imasuangbon ya goyi bayan tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a zabe mai zuwa
  • Yayin da wasu masu fadi a ji a jam’iyyar PDP suke kira ga Atiku akan ya mara wa matasan ‘yan takara daga kudancin kasar nan, a bangaren sa ba haka bane
  • A ranar Alhamis, Imasuangbon ya ce Atiku ne dan takarar da ya fi dace wa ya tsaya a jam’iyyar PDP don a samu nasarar kayar da APC kuma a yi wa arewa adalci

Edo - Wani jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Edo, Barista Kenneth Imasuangbon ya goyi bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya zama dan takarar da PDP zata tsayar a zaben 2023 da ke karatowa, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PDP ta shiga matsi, gwamnonin kudu 3 sun ce ba ruwansu da takarar Atiku

Wasu jiga-jigai na PDP sun yi kira ga Atiku akan ya goyi bayan matasan ‘yan takara daga kudancin Najeriya a kwanakin baya.

Sai dai Imasuangbon a ranar Alhamis ya ce Atiku ne dan takarar da ya fi cancanta PDP ta tsayar don a kayar da jam’iyyar APC a zaben mai zuwa.

2023: Atiku ne zai iya kawo wa PDP nasara, Jigo a Jam'iyyar PDP
2023: JIgo a PDP ya ce Atiku ne zai iya cin zabe a karkashin jam'iyyar. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Imasuangbon ya yi wannan bayanin ne kamar yadda The Punch ta ruwaito ta wata takardar da ya gabatar ga manema labarai a Benin inda ya yi kira ga ‘yan PDP da su goyi bayan Atiku maimakon tallata ‘yan takarar su.

Bisa gogewar Imasuangbon, ya ce Atiku ne ya cancanci takara a 2023

Tsohon dan takarar gwamnan Jihar Edo din ya ce bisa fahimtarsa da gogewarsa ya gane cewa Atiku ya tallafa wa rayuwar mutane da dama a kasar nan.

Kara karanta wannan

Buhari ya sake zabar yar APC a matsayin kwamishinar INEC, HURIWA ta kai kara majalisa

Ya ja kunnen gwamnonin PDP da sauran jiga-jigai da su yi kira ga mabiyansu don mara wa Atiku baya.

A cewarsa:

“Abinda nake so a wurin ‘yan jam’iyyar PDP shi ne mu dage wurin cin zabe. Ba za mu yarda da ‘yan takarar da bamu sani ba.
“Ta ya za ayi mutum ya yi ja in ja akan tsayar da Atiku takara a jam’iyyar nan saboda shekarunsa? Ai tsufa daukaka ce.
“Idan batun adalci ne da gaskiya, ya kamata a mika wa arewa mulki. Shi ne mutumin da yafi dacewa ya yi mulki daga arewa, kada ku manta har yanzu arewa maso gabas bata taba yin shugaban kasa ba.”

Ya ce ba Atiku dama kamar yi wa arewa adalci ne

Kamar yadda yace, tun 1999, kudu ta dinga shugabanci har tsawon shekaru 14 yayin da arewa ta yi shekaru 11 tana shugabanci idan Buhari ya kammala a shekara mai zuwa. Ya kamata a kara wa arewa shekaru 4 don abin ya zama daidai da na kudu.

Kara karanta wannan

Da duminsa:Tsohon shugaban majalisar dattawa ya kuduri aniyar gaje kujerar Buhari

Ya bayyana yadda Obasanjo ya yi shekaru 8, ‘Yar Adua ya yi shekaru 2, Jonathan ya yi shekaru 6. Don haka idan adalci ake so a mayar da mulki arewa.

Kowa ya san Atiku a fadin kasar nan don haka shi ne kadai zai iya kayar da APC a cewar Imasuangbon. Hakan yasa ya bukaci gwamnoni su mara masa baya.

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel