Buhari ya sake zabar yar APC a matsayin kwamishinar INEC, HURIWA ta kai kara majalisa

Buhari ya sake zabar yar APC a matsayin kwamishinar INEC, HURIWA ta kai kara majalisa

  • Bayan an kai ruwa rana, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maye gurbin Lauretta Onochie a matsayin kwamishinar zabe
  • Buhari ya mika sunan Rhoda Gumus, farfesar injiniya a jami’ar Niger-Delta domin majalisa ta tabbatar da ita
  • Sai dai kungiyar kare hakkin dan adam na HURIWA ta yi zargin cewa Gumus ma yar APC ce

Wani rahoton Sahara Reporters ya kawo cewa Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya sake nada yar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a maysayin kwamishinar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.

A watan da ya gabata ne Buhari ya sanar da zabar Rhoda Gumus, farfesar injiniya a jami’ar Niger-Delta domin maye gurbin Lauretta Onochie, hadimarsa a kafofin watsa labarai.

Sauyin ya biyo bayan cece-kucen da zabar Onochie ya haifar, wanda ya ta’allaka ne a kan jam’iyyarta. Don haka majalisar dattawa ta ki amincewa da ita.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sanata ya sanar da kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a 2023

Buhari ya sake zabar yar APC a matsayin kwamishinar zabe - HURIWA
Buhari ya sake zabar yar APC a matsayin kwamishinar zabe - HURIWA Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Amma a ranar 14 ga watan Disamban 2021, Buhari ya nemi majalisar dattawa ta tabbatar da Gumus a matsayin madadin Onochie don zama kwamishinar zabe mai wakiltan kudu maso kudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai, jaridar Sahara Reporters ta ce takardar rijistan Gumus ya tabbatar da ita din yar jam’iyyar mai mulki ce.

Nadin nata ya saba kundin tsarin mulki na 1999 kamar yadda aka gyara ta da dokar zabe.

A cewar takardar,ya zama mambar jam’iyyar APC a ranar 27 ga watan Maris, 2021. Lambar rijistanta shine 58315.

A halin da ake ciki, kungiyar HURIWA ta shigar da korafi mai kwanan wata 26 ga watan Janairu, 2022 dauke da sa hannun jagoranta na kasa, Emmanuel Onwubiko, zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da mataimakinsa, Ovie Omo-agege da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Kara karanta wannan

APC ta rasa wani babban jigonta a majalisar wakilai, ya koma jam’iyyar PDP

Ta bukaci majalisar dokokin tarayyar da ta yi watsi da zabarta don ra’ayin kasa.

Kungiyar kare hakkin ta gargadi majalisar dokokin tarayya a kan tabbatar da Gumus domin kada a haifar da gagarumin rikici na siyasa da ka iya rusa tsarin damokradiyyar kasar.

Buhari zai sake aika wa Sanatoci da sunan Hadimarsa da aka ki amincewa a ba ta mukami

A gefe guda, mun ji a baya mun ji cewa duk da majalisar dattawa ta yi fatali da rokon shugaban kasa na nada Lauretta Onochie a matsayin kwamishinar INEC, watakila a sake aika sunanta.

Punch ta fitar da rahoto a ranar Talata, 13 ga watan Yuli, 2021, ta ce wata majiya dafa fadar shugaban kasa ta shaida mata za a kuma tura sunan Onochie.

Majiyar ta ce har gobe shugaban kasa bai fitar da rai cewa Misis Onochie za ta hau kujerar babbar kwamishina na hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ba.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ba zan bari wani ya hada 'yan daba su dauki makami ba, inji Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel