Neman adalci: Makashin Hanifa ya bayyana a kotu, an dage shari'a zuwa wasu kwanaki

Neman adalci: Makashin Hanifa ya bayyana a kotu, an dage shari'a zuwa wasu kwanaki

  • A yau ne aka gurfanar da mutumin nan da ya kashe dalibarsa bayan sace ta a gaban kotu don amsa laifukansa
  • Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, an zauna a kotu, sannan an saurari lauyoyi kan batun nasa
  • Rahoton ya ce an zauna ne a wata kotun majastare a jihar Kano, wacce ke karkashin alkali Muhammad Jibril

Jihar Kano - Shugaban makarantar Noble Kids da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, Abdulmalik Tanko, ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke jihar Kano.

An gurfanar da shi a gaban babban alkalin kotun, Muhammad Jibril, kan kisan gillar da ya yi wa Hanifa Abubakar, ‘yar shekara biyar, wata dalibarsa da ya sace.

An gurfanar da mutumin da ya kashe Hanifa Abubakar a kotu
Yanzu-Yanzu: An gurfanar da makashin Hanifa Abubakar a wata kotu a Kano | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Abdulmalik ya amsa laifin kashe Hanifa da gubar bera bayan ya sace ta a watan Disamba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kisan Hanifa: Ba zan ɓata lokaci ba wajen zartar da hukuncin kisa kan Tanko, Ganduje

Kafar yada labarai ta BBC Hausa ta rahoto cewa, Abdulmalik ya isa kotun ne tare da wani wanda ake zarginsu da aikata laifin tare.

Waye lauyan da ke tsagin gwamnati?

A cewar rahoto, kwamishinan Sharia na Jihar Kano Barista Musa Lawan ne ke jagorantar lauyoyin gwamnati da ke neman tabbatar da adalci kan kisan Hanifa, wanda shi ne lauya mai gabatar da karar.

Idan baku manta ba, an kama Abdulmalik da wasu mutum biyu, Fatima Jibrin Musa da Hashimu, da laifin hada kai wajen sace Hanifa don neman kudin fansa da kuma kashe ta daga karshe.

Bayan sauraran batutuwa, kotu ta dage zuwa nan da kwana bakwai, inda ake sa ran za a yanke wa wadanda ake zargin hukunci daidai da laifinsu, za a kuma ci gaba da tsare Abdulmalik da abokan harkallarsa.

Kara karanta wannan

Watanni bayan dakatar da ita, Hadiza Bala Usman ta ga shugaba Buhari

A bangare guda, ministan harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, ya bayyana darajar kananan yara yayin da yake martani kan kisan Hanifa Abubakar a Kano.

Ministan, wanda babban malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, ya ce mutane na cin albarkacin kananan yara wajen tausaya musu da Allah ke yi.

A karatunsa na littafin Birrun Walidayya (Biyayya ga iyaye darasi na 12), wanda ya gabatar ranar Lahadi, Pantami yace a ranar Lahira lallashin ƙananan yara ake su shiga Aljanna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel