Ana Wata Ga Wata: Jam'iyyar PDP ta dakatar da Surukin gwamnanta da wasu jiga-jigai uku

Ana Wata Ga Wata: Jam'iyyar PDP ta dakatar da Surukin gwamnanta da wasu jiga-jigai uku

  • Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Benuwai ta dakatar da manyan jiga-jiganta guda huɗu, ciki har da surukin gwamnan jihar, Samuel Ortom
  • Rahotanni sun bayyana cewa APC na ta shirye-shiryen karɓan wasu manyan PDP a jihar, cikin su har da waɗan da aka dakatar
  • Gwamna Samuel Ortom, yace ba zai hana kowa sauya sheka ba, amma ba tantama PDP zata kwace mulki a 2023

Benue - Jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Gwer West, jihar Benuwai, ta dakatar da mambobinta huɗu bisa zargin cin amanar jam'iyya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa waɗan da dakatarwan ta shafa a karamar hukumar sun haɗa da, Surikin gwamna Ortom na jihar Benuwai, Prince Simon Aondoana, tsohon ɗan majalisar tarayya, Chief Goddy Ikyereve, da wasu mutum biyu.

Kara karanta wannan

Mambobin APC mai mulki sama da 11,000 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP

Tutar jam'iyyar PDP
Ana Wata Ga Wata: Jam'iyyar PDP ta dakatar da Surukin gwamnanta da wasu jiga-jigai uku Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Babbar jam'iyyar hamayya ta bayyana cewa dalilin da yasa ta ɗauki matakin dakatar da mutanen shi ne ta gano suna mata maƙarƙashiya.

A halin yanzun, takardar murabus daga jam'iyyar PDP ta mutum biyu daga cikin mutanen, Mista Ikyereve da Mista Aondoana, ta mamaye kafafen sada zumunta.

Wane mataki mutanen suka ɗauka kan dakatar da su?

Jam'iyyar APC ta sanya ranar tarban manyan masu sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP, kuma daga cikinsu har da waɗan da wannan dakatarwan ya shafa.

Daya daga cikin hadiman gwamnan jihar ta ɓangaren yaɗa labaarai, Jimmin Geoffrey, yace an gabatar da lamarin a taron masu ruwa da tsaki na PDP.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya gana da mambobin PDP na yankin karamar hukumar Gwer West a fadar gwamnatinsa dake Makurɗi ranar Litinin.

Kara karanta wannan

APC ta rasa wani babban jigonta a majalisar wakilai, ya koma jam’iyyar PDP

Duk wanda zai fita daga PDP Alla raka taki gona - Ortom

Yayin wannan ganawa, rahoto ya tabbatar da cewa an shaida masa shirin wasu yayan PDP na sauya sheka zuwa tsagin hamayya a jihar.

Da yake martani kan lamarin, Ortom, ya bayyana cewa ba zai ƙalubalanci duk wanda ya yanke hukuncin sauya sheƙa ba, Alla raka taki gona.

Yace duk wani mai hankali da tunani ba zai yi gangancin komawa jam'iyyar APC da ta gaza tsayawa da kafarta ba, inda ya ƙara da cewa ba shakka PDP zata kwace mulki a 2023.

A wani labarin na daban kuma PDP tace tana zargin wasu shugabannin APC da hannu a rura wutar ta'addanci a Najeriya

Jam'iyyar PDP ta bukaci hukumomin tsaro su kira shugabannin APC mai mulki domin amsa tambayoyi kan alaƙa da yan ta'adda.

PDP tace bai kamata jami'an tsaro su kyale ikirarin da tsohon jigon APC ya yi ba kan shigo da yan ta'adda Najeriya a 2015.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun bude wuta, sun yi awon gaba da Kwamishinan Jiha

Asali: Legit.ng

Online view pixel