APC ta rasa wani babban jigonta a majalisar wakilai, ya koma jam’iyyar PDP

APC ta rasa wani babban jigonta a majalisar wakilai, ya koma jam’iyyar PDP

  • Dan majalisa mai wakiltan mazabar Kwami/Funakaye na jihar Gombe a majalisar wakilai, Yaya Tongo ya yi murabus daga jam'iyyar APC
  • Yaya wanda ya sanar da sauya shekarsa a cikin wata wasika zuwa ga shugaban jam'iyyar mai mulki, ya koma PDP
  • Ya ce ya yanke shawarar barin jam'iyyar ne saboda wasu dalilai ciki harda ware shi da aka yi tarukan da ya gudana a kwanan nan

Gombe - Dan majalisa mai wakiltan mazabar Kwami/Funakaye na jihar Gombe a majalisar wakilai, Yaya Tongo, ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasar.

Tongo ya lashe zaben kujerar da yake kai karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2019 da ta gabata.

APC ta rasa wani babban jigonta a majalisar wakilai, ya koma jam’iyyar PDP
APC ta rasa wani babban jigonta a majalisar wakilai, ya koma jam’iyyar PDP Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A cewar wasikar da ya gabatar, dan majalisar ya bayyana wasu kura-kurai da suka hada da fitar da shi daga tarukan da aka gudanar kwanan nan, da kuma kwace jam’iyyar mai mulki da wasu da ba a bayyana ba suka yi a jihar, a matsayin dalilansa na ficewa daga cikinta.

Kara karanta wannan

'Yan sanda da mafarauta sun hallaka 'yan bindiga, sun ceto wasu mutane a Adamawa

Jaridar Punch ta rahoto cewa an sanyawa wasikar da aka aika zuwa ga shugaban jam'iyyar, gudunmar Tongo, dauke da kwanan wata 1 ga Disamba 2021, hannu a ranar 22 ga watan Janairun 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tongo ya kuma bayyana cewa, wasu 'guggun mutane' ne suka kitsa yin watsi da ‘yan jam’iyyar masu daukar nauyinta ta fuskacin kudi, inda ya kara da cewa hakan na da illa ga ci gaban jam’iyyar APC.

Wani bangare na wasikar ya ce:

“Na cimma wannan hukunci nawa ne bayan lura da dimbin rigingimu a cikin jam’iyyar APC ba tare da an shawo kan matsalar ba. Duk kokarin da ‘ya’yan jam’iyyar APC masu kishin kasa ke yi na ganin an shawo kan rikice-rikicen da ake fama da su cikin lumana na ci gaba da fuskantar cikas. Wasu mutane sun kwace dukkan injinan jam’iyyar kuma sun ki ba wasu daga cikin mu damar ba da gudummuwa ga ci gaban APC a jihar Gombe.”

Kara karanta wannan

Labari ne mai ban tsoro - Dattawan arewa sun yi Allah wadai da kisan Hanifa

Da aka tuntube shi don jin ta bakinsa, sakataren APC, Moses Kyari, ya ce kada matakin dan majalisar ya ba masu lura da siyasa a jihar mamaki.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, dan majalisar ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sannan ya karbi katin zamansa cikakken dan jam'iyya ranar Lahadi.

Shugaban kasa a 2023: Tinubu na ci gaba da zawarci, ya ziyarci babban jigo na APC

A gefe guda, babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa, Sanata Sani Musa (APC Neja).

Ziyarar Tinubu na zuwa ne kwanaki uku bayan Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya lamunce ma kudirinsa na neman takarar shugaban kasa.

Sanata Musa na daya daga cikin manyan yan takara da ke neman takarar kujerar shugabancin jam'iyyar APC na kasa a babban taron jam'iyyar mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Daga ƙarshe, Yahaya Bello ya sanar cewa ya shiga jerin masu son gadon kujerar Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel