Zaki ba ya damuwa da kukan tumaki: Bidiyon Tinubu ya na kwasar rawa cikin mata

Zaki ba ya damuwa da kukan tumaki: Bidiyon Tinubu ya na kwasar rawa cikin mata

  • Musiliu Akinsanya wanda aka fi sani da MC Oluomo, shugaban NURTW na jihar Legas, ya ce ya na tsaye gyam bayan Asiwaju Bola Tinubu yayin da ya ke neman shugabancin kasa
  • MC Oluomo wanda ya wallafa bidiyon jigon jam'iyyar APC ya na kwasar rawa, ya kwatanta shi da mutum mai karfi da jini a jika
  • Shugaban NURTW din ya bayyana tabbacin cewa burin Asiwaju Bola Tinubu na zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023 zai cika

Legas - Musiliu Akinsanya wanda aka fi sani MC Oluomo, shugaban kungiyar ma'aikatan sufuri na kasa reshen jihar Legas, ya sha alwashin gooyon bayan burin jigon jam'iyya mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, na zama shugaban kasa.

Zaki ba ya damuwa da kukan tumaki: Bidiyon Tinubu ya na kwasar rawa cikin mata
Zaki ba ya damuwa da kukan tumaki: Bidiyon Tinubu ya na kwasar rawa cikin mata. Hoto daga Musiliu Akinsanya Ayinde
Asali: Facebook

A wallafar da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu, MC Oluomo ya hada Tinubu da kalaman yabo tare da kwarzanta tsohon gwamnan jihar Legas din wanda ya kwatanta da madubin dubawarsa.

Kara karanta wannan

Ban yi wa Buhari kamfen ba, hotunansa kawai na wallafa, Dele Momodu

Hakazalika, ya wallafa bidiyon Tinubu ya na rawa tare da wasu mata inda ya kwatanta jigon APC da "kakkarfa, mai jini a jika, mai dabaru kuma mai son mutane".

MC Oluomo ya rubuta:

"Ga Jagaban ya na yin abin shi. Mutum ne babba wanda ba ya damuwa da duk wasu abubuwan da za su iya dauke masa hankali. Zaki ba ya damun kan sa da ra'ayoyin tumaki.
"Kakkarfa, mai karsashi, dabara, uba da sauransu. A tsaye gyam na ke a bayan ka madubin dubawa na kuma a tare za mu tabbatar da cikar burin ka."

Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu

A wani labari na daban, wani lokacin, ‘yan siyasa su na shirya komai kafin su sauka daga wani mukami wanda daga bisani sai su yi kamar dama faruwa ya yi ba tare da shirinsu ba.

Kara karanta wannan

Abdulsalami: Rawar da Babagana Kingibe ya taka bayan mutuwar MKO Abiola

A ranar Litinin, Asiwaju Bola Tinubu, jigon jam’iyyar APC, ya sanar da manema labarai cewa ya fada wa shugaban kasa Muhammadu Buhari burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa.

Sai dai hakan bai ba jama’a mamaki ba saboda yadda Tinubu ya dade yana kamfen din shugabancin kasa tun kafin ya yi maganar a Aso Rock. Sai dai tambayar da ‘yan Najeriya da dama su ka dinga yi shi ne, “meyasa sai yanzu?”

Asali: Legit.ng

Online view pixel