Daga karshe: Bayan dogon cece-kuce, APC ta saka ranar taron gangami a Fabrairu

Daga karshe: Bayan dogon cece-kuce, APC ta saka ranar taron gangami a Fabrairu

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta tsayar da ranar 26 ga watan Fabrairun bana a matsayin ranar taron gangaminta
  • A baya an samu cece-kuce da rikici a cikin jam'iyyar ta APC kan wannan babban taron gangami da za a yi
  • A baya cikin 2021, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a yi taron gangamin a watan Fabrairun 2022

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da ranar 26 ga watan Fabrairun bana domin gudanar da taron gangaminta na kasa, Vanguard ta ruwaito.

Shugaban kwamitin tsare-tsare na rikon kwarya (CECPC), Gwamna Mai Mala Buni ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja a taron mata da jam’iyyar ta shirya.

Buni ya sanar da ranar taron gangamin APC
Daga karshe: Bayan dogon cece-kuce, APC ta saka ranar taron gangami a Fabrairu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A wurin taron, Buni ya kuma ce, jam’iyyar tana dogaro da goyon bayan mata don gudanar da taron gangamin cikin nasara, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun afil ta zabi ranar zama kan shari'ar dake tsakanin tsagin APC na Shekarau da Ganduje

Gwamnonin APC sun shiga ganawa yayin da rikicin kan taron gangamin jam'iyyar ya kazanta

Kafin sanar da taron gangamin, gwamnoni karkashin jam'iyya mai mulki ta APC sun shiga taro domin neman matsaya kan gangamin taron jam'iyyar da za a yi.

Ana taron ne a masaukin gwamnan jihar Kebbi da ke yankin Asokoro da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Rikici ya na cin jam'iyyar mai mulki tun lokacin da kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ya kasa shirya taron zaben sabbin shugabannin jam'iyyar.

A watan Nuwamban 2021, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da manyan shugabannin jam'iyyar a gidan gwamnati da ke Abuja, inda aka amince kan cewa za a yi zaben sabbin shugabannin jam'iyyar a watan Fabrairu, duk da ba a tsayar da rana ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana fargabar tankar mai ta kashe wasu mutane da dama a wani hadari

A tun farko kunji cewa, jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da ranar da za ta gudanar da babban taronta na gangami a watan Fabrairu, 2022, The Nation ta ruwaito.

Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PGF Gwamna Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin bayan ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Bagudu ya gana da shugaban kasa da shugaban kwamitin rikon kwarya Mai Mala Buni da takwaransa na Jigawa Mohammed Badaru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel