Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari

  • Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya nuna karfin gwiwar cewa za su yi nasara a zabe mai zuwa
  • Ayu ya ce jam'iyyarsa za ta farfado da tattalin arzikin kasar sannan ta kai ta zuwa matakin ci gaba
  • Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Janairu, a yayin wani taron jam'iyyar a jihar Ribas

Rivers - Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya ce babu makawa jam’iyyarsa ce za ta samar da magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ce mulkin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matakin tarayya ya mayar da tattalin arzikin kasar baya kuma cewa ta cancanci a sauya ta.

Ayu ya yi magana ne a wani bikin gala da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya wa gwamnonin PDP a dakin taro na gidan gwamnati da ke Port Harcourt daren ranar Lahadi, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari
Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Ayu ya ce shugabancin APC sun gaza amfani da arzikin yan Najeriya don samar da ingantacciyar rayuwa da za ta karfafa ‘yan uwantaka da inganta zaman lafiya.

Ayu ya ce:

“Abun bakin ciki, lalataccen shugabanci ya raba kan Najeriya sosai a gida da waje.
“Ya zama dole mu sauya wannan labarin kuma hanya daya da za a bi don bunkasa al’ada, muhalli da arzikin da ke kasar shine marawa jam’iyyar Peoples Democratic Party baya don samar da sabon shugabanci a kasar nan.”

Ayu ya bayyana cewa kasar za ta dawo kan kafafunta da jam’iyyar PDP a sama, inda ya bayyana shirin jam’iyyar na maye gurbin Buhari a matsayin wanda za a cimma.

Ya ce:

“Shakka babu PDP za ta samar da shugaban kasa na gaba sannan ta mayar da kasar zuwa lokacin da muke kan mulki, lokacin da muka shafe duk basussukan waje, lokacin da muke bunkasa kasar nan; lokacin da muka zamo kasa mafi arziki a nahiyar Afrika. Amma a yau mune cibiyar talauci a duniya. Duk Wannan zai sauya.”

Kara karanta wannan

Dele Momodu: Allah ne ya tanade ni na gaji Buhari a zaben 2023

Gwamnonin da suka halarci bikin sune Okezie Ikpeazu na Abia, Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa, Udom Emmanuel na Akwa Ibom, Mohammed Bala na Bauchi, Samuel Ortom na Benue, Seyi Makinde na Oyo da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Sauran da suka halarci taron sune mataimakan gwamnonin Ribas da Zamfara, Dr Ipalibo Harry-Banigo da Mahdi Aliyu Mohammed Gudau; sakataren PDP na kasa, Sanata Sam Anyanwu da sauran masu ruwa da tsaki.

2023: Yayin da zabe ke gabatowa, gwamnonin PDP za su gana a Fatakwal, jihar Ribas

A gefe guda, wamnonin Najeriya da ke karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a yau za su yi tar a garin Fatakwal na jihar Ribas domin tsara yadda za su kwace ragamar mulkin kasar nan a shekarar 2023.

Darakta janar na kungiyar gwamnonin, Cyril Maduabum, wanda ya sanar da hakan a ranar Lahadi, ya ce taronsu na farko a sabuwar shekarar zai sake duba halin da jihohin kasar nan, kasar da kuma manyan abokan adawa ke ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Wani na hannun daman saraki ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Ya ce gwamnonin jam'iyyar PDP za su halarci taron wanda zai samu shugabancin shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel