2023: Osinbajo ne ya fi dacewa da takara a APC, ba mu bukatar kuttun kudi, Babangida Aliyu

2023: Osinbajo ne ya fi dacewa da takara a APC, ba mu bukatar kuttun kudi, Babangida Aliyu

  • Tsohon gwamnan jihar Neja, Muazu Babangida Aliyu, ya ce Farfesa Yemi Osinbajo ne ya fi dacewa da takarar shugaban kasa a APC
  • Aliyu ya ce ba su bukatar wani kwashi-kwaraf kuma jakar kudi ya haye ragamar shugabancin kujera mafi daraja ta kasar nan
  • A cewarsa, duk kudin mutum, ko zai fito da dukkan dukiyar da ya mallaka kuma ya karar da ita, ba za su zabe shi ba saboda bai cancanta ba

Tsohon gwamnan jihar Niger, Muazu Babangida Aliyu, ya kwatanta mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da dan takarar da ya fi dacewa da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shugabancin kasa na 2023.

Ya ce duk wani "kwashi-kwaraf ko jakar kudi" ba zai iya kai wa wannan kujerar ba mai daukaka, ko da kuwa kudinsa ya fito da shi, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaman lafiya ya samu: Gwamna Buni ya yabawa Buhari bisa magance rashin tsaro a Arewa

2023: Osinbajo ne ya fi dacewa da takara a APC, ba mu bukatar kuttun kudi, Babangida Aliyu
2023: Osinbajo ne ya fi dacewa da takara a APC, ba mu bukatar kuttun kudi, Babangida Aliyu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Tsohon gwamnan kuma shugaban kwamitin yaraddadu na gidauniyar Sir Ahmadu Bello, ya sanar da hakan ne yayin lakcar shekarar 2022 ta gidauniyar da ake yi a jihar Kano.

"Mataimakin shugaban kasa, ka san cewa kai ne dan takarar da ya fi dacewa da jam'iyyar mu?" yace, yayin da ya ke kwatanta Osinbajo a matsayin dan takarar da ya san kasar nan kuma kowa ya yarje da shi a fadin kasar nan, ba tare da duban kabila ko addini ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce ba za su bar wani "kwashi-kwaraf" ya karba ragamar kasar nan ba ko da kuwa zai fito da dukkan kudin da ya mallaka a duniya.

Ta'adin yan bindiga: Abinda gwamna Masari ya gaya wa Bola Tinubu yayin da yakai masa Ziyara Katsina

Kara karanta wannan

2023: Yayin da zabe ke gabatowa, gwamnonin PDP za su gana a Fatakwal, jihar Ribas

A wani labari na daban, Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, yace gwamnatinsa ta kafa tsarin tsaron ƙauyuka a yaƙin da take domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar, musamman yan bindiga.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakuncin jagoran APC na ƙasa, wanda ya kai ziyarar ta'aziyyar kashe Kwamishina, Rabe Nasir, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

A cewar gwamnan, sabon tsarin da gwamnatinsa ta kafa a ƙauyuka ya ƙunshi sarakunan gargajiya na yankuna, shugaban manyan addinai biyu da suka fi ƙarfi, da kuma shugabannin mahauta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel