2023: Yayin da zabe ke gabatowa, gwamnonin PDP za su gana a Fatakwal, jihar Ribas

2023: Yayin da zabe ke gabatowa, gwamnonin PDP za su gana a Fatakwal, jihar Ribas

  • A yau Litinin, 17 ga watan Janairu ne gwamnonin jam'iyyar PDP za su yi tar a garin Fatakwal da ke jihar Ribas
  • Kamar yadda darakta janar na kungiyar, Cyril Maduabum ya sanar, za su tattauna kan yadda za su kwace mulki ne a 2023
  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesm Wike ne zai zama mai masaukin baki kuma ya shirya kasaitacciyar liyafar dare bayan taron

Gwamnonin Najeriya da ke karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a yau za su yi tar a garin Fatakwal na jihar Ribas domin tsara yadda za su kwace ragamar mulkin kasar nan a shekarar 2023.

Darakta janar na kungiyar gwamnonin, Cyril Maduabum, wanda ya sanar da hakan a ranar Lahadi, ya ce taronsu na farko a sabuwar shekarar zai sake duba halin da jihohin kasar nan, kasar da kuma manyan abokan adawa ke ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun tsaida matsaya kan zaben shugabanni da makomar Buni a taron Abuja

2023: Yayin da zabe ke gabatowa, gwamnonin PDP za su gana a Fatakwal, jihar Ribas
2023: Yayin da zabe ke gabatowa, gwamnonin PDP za su gana a Fatakwal, jihar Ribas. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce gwamnonin jam'iyyar PDP za su halarci taron wanda zai samu shugabancin shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

Maduabum ya ce taron zai kare da liyafar dare wanda babban mai masaukin baki, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike zai dauka nauyi, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce gwamnonin PDP suna aiki tare da tuntubar sauran shugabannin jam'iyyar kuma kwamiti na aiwatar da ayyukan da ke karkashin shugabancin Dr Iyorchia Ayu suna aiki domin ceto Najeriya tare da sauya ta.

"An gayyaci Dr Ayu da ya halarci taron domin tattaunawa da gwamnonin kan yadda za a tsara aikin kwato Najeriya tare da haifar da sabuwar kasa," yace.

Dalilin da yasa na yarda zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Tinubu

A wani labari na daban, babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Bola Tinubu, ya ce da gagarumin goyon bayan jama’a, zai lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu, lokacin da ya ziyarci gidan tsohon gwamnan Oyo, Rashidi Ladoja na Ibadan, jaridar The Cable ta rahoto.

Tsohon gwamnan na Lagas ya bayyana a ranar 10 ga watan Janairu, cewa ya sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari aniyarsa na takarar kujerar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel