Shugabancin 2023: Fastocin kamfen din gwamnan Akwa Ibom sun bayyana a Kano da Jigawa

Shugabancin 2023: Fastocin kamfen din gwamnan Akwa Ibom sun bayyana a Kano da Jigawa

  • Wasu magoya baya sun fara yunkurin don ganin Gwamna Udom Emmanuel ya dare kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
  • A yanzu haka, an gano fastocin yakin neman zaben gwamnan na Akwa Ibom a wasu yankuna na jihohin Kano da Jigawa
  • Fostocin na kuma dauke da logon jam'iyyar PDP mai adawa a kasar

Gabannin zaben 2023, wasu sun fara kokarin ganin gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya shiga tseren kujerar shugaban kasa yayin da fastocin kamfen dinsa suka bayyana a yankuna daban-daban na jihar Kano.

Tuni, wata kungiyar dattawan arewa da na matasa ta nemi a mika shugabancin kasar ga yankin kudancin Najeriya inda ta nemi Gwamna Emmanuel ya nemi kujerar ta daya a kasar.

An gano fastocin da ke ayyana takarar shugaban kasa na Gwamna Udo Emmanuel a tsohuwar birnin Kano, Fagge, karamar hukumar Fagge ta jihar da wasu yankunan jihar Jigawa, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da 1.5m da za a kai Kebbi da Kano

Shugabancin 2023: Fastocin kamfen din gwamnan Akwa Ibom ya bayyana a Kano da Jigawa
Shugabancin 2023: Fastocin kamfen din gwamnan Akwa Ibom ya bayyana a Kano da Jigawa Hoto: Leadership
Asali: UGC

An yi wa fastocin dauke da hoton gwamnan da logon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) take da ‘Udom na zuwa don Najeriya mai inganci’ kuma an manna su a manyan tituna da gine-gine a Kano, Leadership ta kuma rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Emmanuel zai kamala wa’adin mulkinsa na biyu a matsayin gwamnan Akwa Ibom a 2019.

Shugaban kasa a 2023: Shugaban PDP ya yi magana kan magajin Buhari

A wani labarin kuma, Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya ce babu makawa jam’iyyarsa ce za ta samar da magajin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ce mulkin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matakin tarayya ya mayar da tattalin arzikin kasar baya kuma cewa ta cancanci a sauya ta.

Ayu ya yi magana ne a wani bikin gala da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya wa gwamnonin PDP a dakin taro na gidan gwamnati da ke Port Harcourt daren ranar Lahadi, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun tsaida matsaya kan zaben shugabanni da makomar Buni a taron Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel