Hukumar NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da 1.5m da za a kai Kebbi da Kano

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da 1.5m da za a kai Kebbi da Kano

  • Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta kame wasu kayayyaki masu yawa da aka dauko don kawowa Arewa
  • An ce an kama wata motar a jihar Edo ne yayin da ta dauko kayan daga jihar Anambra a yankin kudancin Najeriya
  • Hukumar NDLEA na ci gaba da kame miyagun kwayoyi a yankuna daban-daban na kasar nan a shekarun nan

Abuja - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ta kama kwayoyi akalla miliyan 1.5 na magunguna irin su Tramadol, Exol-5 da Diazepam da aka loda a Onitsha, jihar Anambra.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi, a Abuja, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2022: Gwamnan Plateau zai kashe N100m wajen gyara gidan sauke bakinsa

Jami'an NDLEA sun kama tireloli makare da kwayoyi
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da 1.5m da za a kai Kebbi da Kano | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Twitter

Mista Babafemi ya ce, magungunan da ke kan hanyar zuwa Yauri a jihar Kebbi, hukumar NDLEA ce ta kama su a Edo, a ranar Juma’a 14 ga watan Janairu.

Hakazalika a ranar ne aka gano kwayoyin Diazepam 425,000 a Segemu, Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa, bisa sahihan bayanan sirri, jami’an tsaro a Edo a ranar Juma’a 14 ga watan Janairu sun kama wata tirela da ta taho daga Onitsha zuwa Yauri a jihar Kebbi.

A cewar sanarwar:

“Magungunan da aka kama sun hada da: kafso 394,480 da kwayoyin Tramadol 3,000 masu nauyin kilogiram 83.707; Exol-5: kwayoyi 647,500 masu nauyin 203.315kg; Diazepam: kwayoyi 12,500 masu nauyin 2.05kg."

Bugu da kari, akwai:

“Bromazepam: Kwayoyi 1,500 masu nauyin 0.45kg; Maganin ruwa na Codeine: kwalabe 999 masu nauyin 134.865kg; Alluran Pentazocine: 4,000 masu nauyin kilogiram 16.64."

Kara karanta wannan

Daukar aiki: Bayan shekaru biyu ana jira, NSCDC ta gayyaci mutum 5000 a cikin miliyan 1.5

Mista Babafemi ya ce an kama direban motar, Bashir Lawali mai shekaru 30 tare da Abubakar Sani mai shekaru 30 da kuma Ali Abubakar mai shekaru 19.

An kuma kwace kayayyakin kwayoyin na Kano daga hannun wani Sa’idu Yahya mai shekaru 31, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

A halin da ake ciki, jami’an NDLEA sun dakile yunkurin da masu safarar miyagun kwayoyi ke yi na fitar da fakiti 73 na tabar wiwi (34.05kg) da aka boye a cikin kwantenar abinci zuwa kasar Burtaniya.

Kwastam ta yi babban kamu, ta kame kwantena makare da tramadol na biliyoyi

A wani labarin, Rundunar Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), sashen Seme, ta ce ta kama wasu kayayyaki da ake zargin kwayoyin tramadol ne da aka boye cikin manyan kunzugun yara a cikin kwantena.

Kayayyakin suna da darajar kudi akalla na Naira biliyan 1.4 da aka lissafa su, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: NDLEA ta titsiye biloniya Obi Cubana kan zargin safarar miyagun kwayoyi

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Kwastam Hussain Abdulahi, a wata sanarwa da ya fitar a Seme, ya ce lambar kwantenar ita ce MRKU 9090415.

Asali: Legit.ng

Online view pixel