Dalilin da yasa kaso biyu cikin uku na yan majalisa ba za su samu komawa zauren ba

Dalilin da yasa kaso biyu cikin uku na yan majalisa ba za su samu komawa zauren ba

  • Kamar yadda yake bisa al'ada, ba dukka yan majalisa bane za su samu damar komawa kujerunsu ba a zaben 2023
  • Wasu gazawarsu ce za ta hana masu komawa kan kujerar yayin da wasu kuma za su samu cikas ne saboda rikicin cikin gida a matakin jiha
  • Hakazalika wasu za su bar kujerunsu na majalisa ne domin neman takarar wasu kujerun na daban kamar irin kujerar gwamna

Dabi'ar nan da kaso 67 cikin dari na yan majalisar dokokin tarayya basa samun damar komawa zauren bayan kowani zabe na shirin ci gaba a 2023 yayin da yan majalisa masu ci ke kara samun cikas.

Babban cikas da yan majalisar suka samu shine rashin nasara a yunkurinsu na tilastawa jam'iyyun siyasa amfani da tsarin zaben fidda gwani na kai tsaye a wajen tsayar da yan takararsu.

Kara karanta wannan

Dattawan arewa sun bayyana manyan sharudda 3 don marawa yan takarar shugaban kasa baya a 2023

Akwai kuma rikice-rikice na cikin gida da suka haifar da bangarori a cikin jam'iyyu a matakin jiha, wanda hakan na iya kawo matsala a sakamakon zabe mai zuwa.

Sannan kuma wasu yan majalisa na shirin neman takarar wasu kujeru daban wanda hakan zai hana masu komawa kujerarsu ta majalisar.

Dalilin da yasa kaso biyu cikin uku na yan majalisa ba za su samu komawa zauren ba
Dalilin da yasa kaso biyu cikin uku na yan majalisa ba za su samu komawa zauren ba Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Misali a zaben 2015, sanatoci 70 cikin 109 basu samu komawa majalisar dattawa ba yayin da mambobin majalisar wakilai fiye da 250 suka rasa kudirinsu na komawa kujerunsu.

Yawan adadin ya dan yi dama-dama a 2019 inda sanatoci 45 da yan majalisar wakilai 209 suka samu komawa majalisar dokokin.

An kirkiri shirin gyara dokar zaben na 2010 a 2021 domin ya ba yan majalisar damar fafatawa da ka'idojin gwamnonin jiha wadanda ke jan ragamar jam'iyyar. Sai dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da dokar a shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Hular Tinubu ta yi daraja a kasuwar intanet, 'yan Najeriya sun yi tururuwa domin saye

Jaridar Leadership ta rahoto cewa akalla sanatoci 18 ne suke shirin janyewa daga sake takarar kujerunsu a 2023; maimakon haka suna hararar kujerar gwamna a jihohinsu mabanbanta.

Wadannan sun hada da sanatocin Taraba, Bauchi Kano, Plateau, Rivers, Delta, Cross River, Abia, Ebonyi, Ekiti and Oyo.

A Taraba, dukka sanatocin jihar uku ne suke son darewa kujerar gwamna, yayin da a Bauchi Delta, Cross River da Oyo, akwai a kalla sanatoci biyu da ke hararar kujerar.

Sannan a Ekiti inda za a yi zaben gwamna a watan Yunin 2022, dole ne yan takarar da ke neman kujerar su hakura da kujerunsu na majalisa.

A yanzu da aka gaza samun nasarar yiwa dokar zaben gyara, hakan na nufin duk dan takarar da ke neman sake mallakar tikitin jam'iyyar sai ya bi ta gidan gwamnati a jiharsa.

A wasu wuraren ma, gwamnonin da kansu ne ke neman shigewa majalisar dattawa yayin da hadimansu ke yakin neman kujerun majalisar wakilai. Hakan na nufin suna son maye gurbin mambobin majalisa masu ci a yanzu.

Kara karanta wannan

Yan siyasar kudu maso gabas 5 da ake sa ran za su fafata a zaben shugaban kasa a 2023

Shugaban kasa a 2023: IBB ya bayyana wanda zai iya gadar shugaba Buhari

A wani labarin, tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya jadadda matsayarsa kan cewa ba zai marawa tsoho baya ba a zaben shugaban kasa na 2023.

A wata hira da yayi da jaridar Daily Trust a baya-bayan nan, IBB ya jero wasu sharudda da suka zama dole duk mai neman kujerar shugaban kasa a 2023 ya cike.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa ba zai taba marawa wanda ya haura shekaru 60 baya don zama shugaban kasa ba, rahoton PM News.

Asali: Legit.ng

Online view pixel