Yanzu-Yanzu: Tsohon gwamna, kuma jigon APC a Oyo ya riga mu gidan gaskiya

Yanzu-Yanzu: Tsohon gwamna, kuma jigon APC a Oyo ya riga mu gidan gaskiya

  • Rahoton da ke fitowa daga majiyoyi ya bayyana cewa, tsohon gwamnan jihar Oyo, Otunba Adebayo Alao-Akala ya riga mu gidan gaskiya
  • Rahotanni sun ce ya rasu ne da sanyin safiyar yau Laraba, 12 ga watan Janairun wannan shekarar ta 2022
  • Ya zuwa yanzu dai babu wasu cikakkun bayanai kan mutuwarsa, domin majiya bata bayyana jawabi daga danginsa ba

Ogbomoso, Oyo - Wani tsohon gwamnan jihar Oyo, Otunba Adebayo Alao-Akala, ya rasu da sanyin safiyar Laraba a Igbomoso.

Akala, jigo a jam’iyyar APC, ya kasance tsohon gwamnan jihar, tsakanin 2007 zuwa 2011, Vanguard ta rahoto.

Jihar Oyo ta yi rashin tsohon gwamna
Da dumi-dumi: Tsohon gwamnan jihar Oyo ya riga mu gidan gaskiya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya kuma kasance mataimakin gwamna a karkashin tsohon gwamna, Rashidi Ladoja tsakanin shekarar 2003 zuwa 2006, lokacin da aka tsige Cif Ladoja, wanda a sakamakon haka ya zama gwamnan rikon kwarya na tsawon watanni goma sha daya.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi na wani tsohon shugabanta

Gwamnan Oyo Seyi Makinde ya tabbatar da mutuwar magabacin nasa Otunba Adebayo Alao-Akala.

Makinde ya bayyana haka ne a lokacin da aka kira shi da ya yi jawabin fatan alheri a ci gaba da gudanar da addu’o’in mabiya addinai na ma’aikatan Oyo.

Gwamnan ya ce ya samu labarin ne yayin da yake cikin taron, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Tsohon shugaban kasa a Najeriya Ernest Shonekan ya rasu

A wani labarin, Cif Ernest Shonekan wanda ya jagoranci gwamnatin rikon kwarya wacce ta gaji mulkin Janar Ibrahim Babangida, ya rasu.

Shonekan ya rasu a jihar Legas yana da shekaru 85 a duniya, kamar yadda The Guardian ta rahoto.

Ya kasance shugaban kasa Najeriya na wucin gadi tsakanin 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamba, 1993 lokacin da aka hambarar da shi a juyin mulkin da marigayi Janar Sani Abacha ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin sanatoci 13 a Najeriya da ke neman kujerar gwamna a jihohinsu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel