Batun kasafin kudin 2023: Buhari ya ce ba za a samu matsala ba saboda APC

Batun kasafin kudin 2023: Buhari ya ce ba za a samu matsala ba saboda APC

  • Majalisar dokokin kasar nan za ta aiwatar da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2022 da shugaban kasa ya sanya wa hannu
  • Wannan ne kwarin guiwar shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin wata hira da aka yi da shi a ranar Alhamis, 6 ga watan Janairu
  • Shugaba Buhari ya ce ya amince da shugabannin jam’iyyar APC a majalisar dokoki da su yi aiki mai kyau kan kasafin kudin 2022

Abuja - Shugaba Buhari ya bayyana cikakken jin dadi da kwarin gwiwarsa kan cewa ba za a samu matsala wajen aiwatar da kasafin kudin kasar na 2022 ba.

Shugaban kasar, a wata hira da yayi da gidan Talabijin na NTA, ya bayyana cewa amannar da yake da ita ta samo asali ne daga yadda jam'iyyar APC ke jagorantar majalisar.

Kara karanta wannan

Na kusa da Jonathan ya bayyana matsayar tsohon shugaban kan tsayawa takara a 2023

A baya shugaban kasan da gwamnatinsa sun sha fama kan yadda majalisun kasar ke walagigi da kasafin kudin kasar.

Shugaban Najeriya Buhari ya maganti kan kasafin kudin 2022
Kasafin kudin 2023: Buhari ya ce ba za a samu a matsala a Najeriya ba saboda APC | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Ya kuma yi alfahari da cewa cancantar manyan ‘yan majalisa irin su shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da shugaban majalisar Femi Gbajabiamila ne yasa za a iya amincewa da aiwatar da kasafin kudin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban ya ce:

“Amincin da nake da shi cewa za mu yi nasarar aiwatar da kasafin kudin shi ne, saboda a majalisun biyu, jam’iyya ce ke kan gaba.
“Jam’iyyar APC ce da shugabanci; dubi Shugaban Majalisar Dattawa, ya kasance a Majalisar Wakilai na tsawon wa’adi biyu zuwa uku kafin ya je Majalisar Dattawa.
“Ku dubi Femi Gbajabiamila, ina kallon talabijin, a lokacin da yake mamba gama gari, kullum yana kan kujerarsa yana yaki saboda jam’iyya da tsarin da muka yi imani da shi.

Kara karanta wannan

Bashin China: Ko yanzu muke bukatar bashi, za mu sake karbowa, Buhari

“Hakika, ina ganin kaina mai sa’a. Jam’iyyata da kwararrun shugabancinsu duk suna kan gaba a majalisar dattawa da ta wakilai.”

'Yan Majalisar Wakilai sun amince da Kasafin Kudin 2022, sun kara N700bn

Majalisar wakilan tarayya a ranar Talata, 21 ga Disamba 2021, ta amince da daftarin kasafin kudin 2022 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar mata a watan Oktoba.

Maimakon N16.39tr da Buhari ya gabatar, yan majalisan sun kara sama da bilyan 700 kai zuwa N17.126 trillion.

ChannelsTV ta ruwaito cewa majalisar ta kara N400bn wa ma'aikatu irinsu INEC, Majalisar dokoki da ma'aikatar tallafi da jin kai, dss.

Majalisa kuma ta kara kiyasin farashin danyen mai daga $57/ganga zuwa $62/ganga.

A wani labarin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu wanda ake zargi da cin hanci da rashawa da zai tsira saboda ya koma jam’iyyarsa ta APC, Premium Times ta tattaro.

Buhari ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na NTA a ranar Alhamis 6 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Neman zaman lafiya: Shugaba Buhari ya jaddada kudurinsa na samar burtali ga Fulani

‘Yan Najeriya da dama na ganin cewa ‘yan siyasa a tsagin adawa da ake zargi da cin hanci da rashawa ko kuma aka gurfanar da su a gaban kuliya bisa zargin cin hanci da rashawa suna kaura zuwa jam’iyyar APC ne don gudun kada a hukunta su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel