Na kusa da Jonathan ya bayyana matsayar tsohon shugaban kan tsayawa takara a 2023

Na kusa da Jonathan ya bayyana matsayar tsohon shugaban kan tsayawa takara a 2023

  • Cif Dikivie Ikiogha, na kusa da Goodluck Jonathan ya magantu a kan matsayar tsohon shugaban kasar na tsayawa takara a zaben 2023
  • Ikiogha ya ce sam Jonathan bai amince da shiga tseren kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa ba
  • Ya yi watsi da rahoton da ke yawo a kafafen yada labarai, inda ya bayyana hakan a matsayin makirci

Bayelsa - Wani makusancin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kuma jJagoran kungiyar masu fafutukar shugabancin Kudu maso Kudu a 2023, Cif Dikivie Ikiogha, ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan bai amince da yin takarar shugaban kasa ba.

Ya kuma yi watsi da rahotannin kafafen sada labarai cewa taron da kungiyar tayi da Jonathan a Yenagoa don shirya dabarun komawarsa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) don cimma kudirinsa na zama shugaban kasa, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Jonathan ya ziyarci Buhari a Aso Rock, ya yi masa bayani kan rikicin Mali

Na kusa da Jonathan ya bayyana matsayar tsohon shugaban kan tsayawa takara a 2023
Na kusa da Jonathan ya bayyana matsayar tsohon shugaban kan tsayawa takara a 2023 Hoto: John Kalapo
Asali: Getty Images

Ikiogha, wanda ya kafa kungiyar, ya fada ma manema labarai a Yenagoa, cewa makirci ne kafafen yada labarai su rahoto cewa kungiyar sun gana da Jonathan ne domin su tsara dabarun mayar da shi kan kujerar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC.

Hadimin na Jonathan wanda ya kuma kasance mamba na APC reshen jihar, ya ce ziyarar da suka kai wa tsohon shugaban kasar kamar wasu da dama suka yi, ya kasance don sanar da shi shirin kungiyar da dalilansu na kira ga shugabancin kudu maso kudu a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ikiogha ya ce:

"Rahoton bai yi wa kungiyarmu adalci ba. Bai kuma yi wa Dr. Goodluck Jonathan adalci ba. Wannan ba aikin jarida na binciken kwakkwafi bane. Abu ne da suka kulla sannan suka je kafar watsa labarai da shi. Da ace suna son aikin jarida na gaskiya, da za su tuntube ni sannan su san matsayin kungiyarmu kafin su wallafa labarin.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Wasu jiga-jigan PDP a jihohi 24 sun zabi Atiku ya gaji Buhari, inji Dokpesi

"Ayyukanmu da hakokin da suka rataya a wuyanmu a bayyane suke a kundin tsarin mulkin mulkin shugabancin kudu maso kudu na 2023. Mu kungiyar fafutuka ne kuma ba za mu dunga magana a iska ba batare da mun yi tuntuba da ganawa da mutane ba.
"Mun hadu da mutane da dama amma ba a ce za su yi takarar zabe ba. Tsawon sama da shekara daya, muna ta aiki amma ziyara daya da muka kaiwa Jonathan, an fassara shi baibai. Sun yi ikirarin cewa Jonathan ya yarda yayi takarar shugaban kasa.
“Jonathan bai yarda ya tsaya takara ba kuma ba mu je wurin don mu lallashe shi ya tsaya takara ba. Mun gaya masa cewa mu kungiya ce mai fafutukar neman shugabancin kudu maso kudu. Kuma cewa mun dade muna magana kuma dole ya sha karanta abubuwa kanmu.
"Mun gaya masa cewa abin da kungiyar ke so shi ne shugaban kasar Najeriya na gaba ya fito daga Kudu maso Kudu."

Kara karanta wannan

Ba matsala bane musulmi da musulmi su gaji Buhari da Osinbajo, inji kungiyar magoya bayan Tinubu

Da an ji kunya: Bai dace APC ta ba Jonathan takarar shugaban kasa ba - Tsohon Hadimin Buhari

A gefe guda, tsohon ‘dan majalisar tarayya, Hon. Abdurrahman Kawu Sumaila yace makiyan APC ne suke shirin ba Goodluck Jonathan takarar jam’iyya a 2023.

Daily Trust ta rahoto Honarabul Abdurrahman Kawu Sumaila yana cewa tsohon shugaban Najeriyar ya yi iya yinsa, ya kamata a kyale shi ya huta kuma.

Kawu Sumaila ya na ganin jam’iyyar APC ta na da ‘yan takarar shugaban kasa daga kudancin Najeriya da suka fi Goodluck Jonathan cancanta da samun tikiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel