Zan sa kafar wando daya da kai, Mataimakin gwamna ya aike da zazzafan sako ga gwamnansa

Zan sa kafar wando daya da kai, Mataimakin gwamna ya aike da zazzafan sako ga gwamnansa

  • Sabon rikici ya barke tsakanin gwamna Matawalle na jihar Zamfara da kuma mataimakinsa, Mahdi Aliyu
  • Mataimakin gwamnan ya sha alwashin sa kafar wando ɗaya da uban gidan na sa saboda rashin adalcin da ake wa PDP a jihar
  • Ya roki gwamna Matawalle ya maida hankali kan kalubalen da jihar Zamfara ke fama da su, ya bar PDP ta gudanar da harkokinta

Zamfara - Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Aliyu, yace ya shata layin faɗa tsakaninsa da uban gidansa, gwamna Bello Matawalle.

Da yake jawabi a karshen taron jam'iyyar PDP na jiha ranar Litinin da daddare, mataimakin gwamnan yace babu sauran ɗaga kafa tsakanin su, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Matawalle da Mahdi Aliyu
Zan sa kafar wando daya da kai, Mataimakin gwamna ya aike da zazzafan sako ga gwamnansa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mataimakin gwamnan yace:

"Daga yau mun sa kafar wando ɗaya, zamu ɗaga murya idan gwamnati ta yi shiru. Matukar gwamnatin Zamfara ta ki buɗe makarantu, zamu ɗaga murya."

Kara karanta wannan

Ta kacame tsakanin 'yan siyasar Zamfara bayan 'yan daba sun hargitsa taron PDP

"Ba zamu yi shiru ba idan manoma ba su samun damar zuwa gonakin su, ko kuma aka ƙi gina wa mutane hanyoyi.
Daga yanzu, har zuwa lokacin da gwamnati zata dawo hannun mu, ba zamu yi shiru ba, za mu cigaba da caccakar kudirorin gwamnati mara sa kyau."

Wane hali PDP take ciki a jihar Zamfara?

Mista Aliyu ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake zaluntar jam'iyyar PDP a jihar Zamfara tun bayan sauya shekar Matawalle zuwa APC mai mulki.

Mataimakin gwamnan yace PDP na bin dukkan dokoki, kuma kundin tsarin mulkin ƙasa ya baiwa jam'iyyar yancin cigaba da harkokinta a Zamfara.

Kazalika ya sha alwashin gina sabuwar PDP a jihar Zamfara ta hanyar amfani da matasa masu basira da hazaƙa.

"Wannan zai baiwa PDP damar kwace mulki a jihar bayan babban zaɓen 2023 dake tafe."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan sanda sun sako sirikin Sanata Okorocha da suka cafke

Ka maida hankali kan tsaro - Aliyu

Aliyu ya roki gwamnan ya fita daga harkokin jam'iyyar PDP, ya maida hankali kan magance ƙalubalen da jihar Zamfara ke fama da su.

Haka nan kuma ya yi kira ga gwamnan ya samar da ayyukan cigaba ga jihar, inda yace, "Har yanzun ilimin kananan yara masu ta so wa na nan yadda yake."

A wani labarin na daban kuma Hotunan yadda yan daba suka yi fata- fata da wurin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara

Wasu gungun yan daban siyasa sun farmaki filin da PDP ta shirya gudanar da zaɓen shugabanninta a matakin jiha a Zamfara.

Rahotannu sun bayyana cewa yan daban sun farfasa motoci, sun lalata runfunan da aka kafa, kuma sun yi kone-kone.

Asali: Legit.ng

Online view pixel