Bayan shekaru 6, gwamnatin Katsina ta bayyana lokacin da za ayi zaben kansiloli

Bayan shekaru 6, gwamnatin Katsina ta bayyana lokacin da za ayi zaben kansiloli

  • Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana lokacin da za a gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar
  • Jihar Katsina dai ta ruguje kujerun kansila a jihar tun bayan da ta zargi karkatar da kudin al'umma a bangaren
  • A yanzu gwamnati ta ce ta shirya komai tsaf domin gudanar da wannan zabe a kwatan farko na shekara mai zuwa

Jihar Katsina - Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Katsina ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a cikin kwatan farko na shekara mai zuwa.

Gwamna Aminu Masari na jihar ne ya bayyana hakan a jiya a wata hira da manema labarai, ya ce an samar da 70% cikin 100% na abin da ake bukata na zaben.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari
Katsina ta bayyana lokacin zaben kananan hukumomi duk da matsalar tsaro | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Karo na karshe da aka gudanar da zaben kansiloli shi ne sama da shekaru shida da suka gabata, a lokacin mulkin karshe na jam’iyyar PDP na tsohon Gwamna Ibrahim Shema.

Kara karanta wannan

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja

Amma Masari, wanda ya zama gwamna a jam’iyyar APC, ya rusa kujerun kansiloli ne a watan Mayun 2015, saboda zargin karkatar da dukiyar al’umma a matsayin dalilin yin hakan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masari ya ce an kafa wani kwamiti a karkashin shugaban ma’aikatansa, Muntari Lawal da zai yi aiki tare da masu ruwa da tsaki domin gudanar da zaben.

Ya ce:

“Kashi 70 na abin da ake bukata domin zaben yana nan a kasa, kuma muna fatan gudanar da zaben a cikin kwatan farko na shekara mai zuwa.”

Ya ce an samu jinkirin gudanar da zaben ne saboda shari’ar kotu da PDP ta shigar, kuma gwamnati ba ta so a ci gaba da gudanar da zaben ba saboda shari’ar da ake yi a lokacin.

Jaridar Punch ta ce Masari ya kara da cewa gwamnatinsa ta duba tare da sake tantance ma’aikatan kananan hukumomi sama da mutum 2,000 wadanda a baya gwamnatin da ta shude ta hana su albashi.

Kara karanta wannan

Coca Cola ta kaddamar da 'Project EQUIP' a Kano: Ga Muhimman abubuwa 3 da shirin zai mayar da hankali a kai

Masari ya kuma ba da shawara kan zaben 2023, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki su sanya Najeriya a gaba akan komai na ayyukansu.

Ya ci gaba da cewa:

“Yayin da muke fuskantar zabukan 2023, ina kira ga shugabanni, galibinsu na addini, na gargajiya, da shugabannin siyasa a kasar nan da su sanya kasar nan a gaba."

Ku sayi bindiga, ku kare kan ku: Masari ya yi kira ga al'ummar jiharsa

A wani labarin, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi kira ga al'ummar jiharsa su mallaki makamai don kare kansu daga hare-haren yan bindiga saboda jami'an tsaro kadai ba zasu iya ba.

Masari, wanda ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Muhammadu Buhari House dake Katsina ya ce adadin jami'an tsaron da Najeriya ke da shi ya yi kadan wajen magance wannan matsala.

A cewarsa, ko addini ya amince da mutum ya kare kansa da dukiyarsa daga wanda ke kokarin kwacewa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja ta kama almajirai 104 masu kananan shekaru da aka shigo dasu

Asali: Legit.ng

Online view pixel