Kisan Kaduna: Ku karar min da ragowar 'yan ta'adda, Buhari ga hukumomin tsaro

Kisan Kaduna: Ku karar min da ragowar 'yan ta'adda, Buhari ga hukumomin tsaro

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan jama'a da 'yan ta'adda ke yi a yankunan jihar Kaduna
  • Kai tsaye Buhari ya kwatanta makasan da 'yan ta'adda kuma ya yi kira ga hukumomin tsaro da su karar da ragowar 'yan ta'addan
  • Buhari ya ce ya shiga matsanancin tasin hankali kan kisan inda yace radadin wutar da jami'an tsaro suke sakarwa 'yan ta'addan ne suke hucewa kan jama'a

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren kwanan nan da 'yan bindiga ke kai wa Kaduna, inda ya kwatanta su da 'yan ta'adda.

Rayuka talatin da takwas aka tabbatar da mutuwarsu bayan farmakin da 'yan bindiga suka kai wasu yankuna da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya magantu kan karuwar rashin tsaro, ya aike wa 'yan Najeriya muhimmin sako

Wannan lamarin na zuwa ne bayan kwanaki kadan da kotu ta ayyana kungiyoyin 'yan bindigan da 'yan ta'adda.

A wata takarda da Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Facebook, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce, Buhari ya ce maharan suna "jin radadin zafin" ayyukan cikin kwanakin nan da jami'an tsaro ke yi, hakan yasa suke kai wa yankuna farmaki.

Kisan Kaduna: Ku karar min da ragowar 'yan ta'adda, Buhari ga hukumomin tsaro
Kisan Kaduna: Ku karar min da ragowar 'yan ta'adda, Buhari ga hukumomin tsaro. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ya umarci hukumomin tsaro da su tsananta ayyukansu ta yadda za su karar da ragowar 'yan ta'addan.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kushe sabon harin 'yan ta'adda inda suka halaka mutane a jihar Kaduna. Ya ce kisan gillar da aka yi a Kauran Fawa, Marke da Ruhiya na Idasu a karamar hukumar Giwa ya tsunduma shi cikin bakin ciki kuma ba za a lamunci irin wannan kisan ba," takardar tace.

Kara karanta wannan

Kungiya Ta Yi Kira Ga 'Yan Kudancin Najeriya Su Saka Baki Don Kawo Ƙarshen Kashe-Kashe a Arewa

"A cikin makon nan 'yan bindiga sun kashe jama'a a Zangon Kataf, Chikun, Birnin Gwari, Igabi da Kauru duk a jihar Kaduna,
“Shugaban kasa Buhari ya tabbatar da cewa, jami'an tsaro suna sakar wa 'yan ta'addan wuta, hakan yasa suke sauke fushinsu kan jama'a inda suke kisa, satar kadarori, kone gidaje da sauransu.
"Ya jaddada umarninsa ga shugabannin tsaro da na sirri da su yi duk abinda ya dace wurin ganin sun karar da ragowar 'yan ta'addan."

Shugaban kasar ya kara da mika ta'aziyyarsa ga jama'ar jihar Kaduna da na masarautar Zonkwa kan mutuwar Nuhu Bature, Agwam Kajju.

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mulkinsa ba zai huta ba har sai kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta a yanzu ta kawo karshe, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sarki a arewacin Najeriya ya koka kan kwace masarautarsa da 'yan bindiga suka yi

Buhari, wanda ya samu wakailcin ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonayan Onu, ya sanar da haka ne a yayin gabatar da wani littafi mai suna "Standing Strong" wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya rubuta a Abuja.

"Muna cigaba da duba hanyoyi da tsarikan cigaba da nakasa dukkan wani karfin 'yan ta'adda a kasar nan," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel