Takarar 2023 na neman raba kan Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Ubangidansa, Tinubu

Takarar 2023 na neman raba kan Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Ubangidansa, Tinubu

  • Tun kafin a fara buga gangunan zaben 2023, wasu magoyan baya sun dukufa da yakin neman zabe
  • Masu goyon bayan Farfesa Yemi Osinbajo su na ta kira ya tsaya takarar shugaban Najeriya a 2023
  • Haka zalika akwai kungiyoyin da ke tare da Asiwaju Bola Tinubu da ke zuga shi ya nemi shugabanci

Magoya bayan babban jagoran jam’iyya APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu da na mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo su na ta kamfe tun yanzu.

Jaridar Daily Trust tace bangarorin biyu duk sun dage da shirin yakin neman zaben shugaban kasa, duk da cewa har yanzu lokacin neman takaran bai yi ba.

Yemi Osinbajo bai fito ya bayyana niyyarsa na neman zama shugaban kasa a 2023 ba. Amma akwai wasu dinbin magoya bayan da ke cin albasa da bakinsa.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

Haka lamarin yake ga tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu wanda shi ma wasu kungiyoyi suke.

Sarkin Daura ya nuna wanda ya dace - PCG

Irinsu kungiyar PCG su na ganin Osinbajo ya dace ya karbi ragamar mulki. Blue Print ta rahoto kakakin kungiyar, Emmanuel Pippa ya na jaddada wannan batu.

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Ubangidansa, Tinubu
Farfesa Osinbajo da Bola Tinubu Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Barista Pippa yace ganin yadda Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk ya yabi Osinbajo, ya nuna babu wanda ya kamata ya gaji Muhammadu Buhari irinsa.

The Disciples of Jagaban ta fara kamfe a Kaduna

Rahoton yace a jihar Kaduna, Sanata Mohammed Saleh da mutanensa na The Disciples of Jagaban na cikin masu marawa Tinubu baya ya nemi takara a 2023.

Tsohon sojan yana cikin wadanda suka gana da Tinubu tare da Janar H. Usman, Muhammad Namadi, Alhaji Dangulguli, da Alhaji Lawal Meyere na kungiyar ACF.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gana da wasu ‘Yan Arewa, ya fadi abin ya ke jira ya ayyana takarar Shugaban kasa

Tinubu ya hakura kawai inji Osita Okechukwu

A daidai wannan lokaci sai aka ji darekta janar na hukumar VON, Osita Okechukwu, ya na ba Tinubu shawarar ya janye batun takara, ya marawa matashi baya.

Jaridar The Cable ta rahoto Osita Okechukwu ya na cewa bai dace Tinubu ya nemi mulki ba.

Ra’ayin Tinubu a kan batun zaben shugaban kasa

A makon jiya aka ji tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zauna da ‘Yan kungiyar Northern Alliance Committee a birnin tarayya Abuja.

‘Dan siyasar ya shaidawa magoya bayansa cewa ba zai ba su kunya a 2023 ba. A game da batn takara, Tinubu yace ya na tuntubar abokan tafiyarsa ne a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel