Rikici ya zo karshe: Jam'iyyar APC ta kafa kwamitocin gangamin taro na ƙasa

Rikici ya zo karshe: Jam'iyyar APC ta kafa kwamitocin gangamin taro na ƙasa

  • Jam'iyyar APC ta ƙasa ta fara shirye-shiryen gangamin taronta na ƙasa ta zata gudanar a watan Fabrairu, 2022
  • A taron da kwamitin rikon kwarya ta APC ta ƙasa ta gudanar, ya yanke kafa kwamitoci daban-daban game da taron
  • APC ta kuma mika sakon godiya ga yan Najeriya da kuma yi musu fatan gudanar da shagalin kirsimeti lafiya

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta sanar da cewa ta yanke hukuncin kafa kwamitin kasafi da sauran kwamitoci gabanin babban taronta na ƙasa a watan Fabrairu.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan taron kwamitin rikon kwarya, sakataren APC na ƙasa, Sanata James Akpanudoedehe yace kwamitinsu ya sake nazari kan ayyukan da ya gudanar tsawon shekara daya.

Dailytrust ta ruwaito cewa taron mambobin kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC ta ƙasa ya gudana ne ranar Litinin a sakateriyarta dake Abuja.

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyyar APC a jihar Kano ba zai raba mun hankali ba, Gwamna Ganduje

Kwamitin Buni
Rikici ya zo karshe: Jam'iyyar APC ta kafa kwamitocin gangamin taro na ƙasa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A baya-bayan nan ne jiga-jigan APC na ƙasa suka gana da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a gidan gwamnatinsa Aso Rock.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin wannan ganawa ta su ne, suka amince da cewa za'a gudanar da babban taron APC na ƙasa a watan Fabrairu, amma ba su zaɓi rana ba.

Me suka tattauna a wannan taron?

Kazaika a taron kwamitin (CECPC) na yau ƙarƙashin jagorancin gwamna Mala Buni, ya gaza sanar da ainihin ranar da taron zai gudana a watan Fabrairu.

Punch ta rahoto Akpanudoedehe yace:

"A taron kwamitin rikon kwarya (CECPC) na APC karo na 18 da ya gudana a sakateriyar jam'iyya ta ƙasa ranar 20 ga watan Disamba ya yi duba zuwa ga ayyukan da ya gudanar tsawon shekara ɗaya."
"Kwamitin ya kuma tattauna kan batutuwa da dama kuma ya cimma matsaya kamar haka: Game da taro na ƙasa an yanke kafa kwamitin kasafin kudi da sauran kwamitin da suka shafi taron."

Kara karanta wannan

2023: Kada ku sake kuskuren amincewa da jam'iyyar PDP, Shugaban Majalisa ya roki matasan Najeriya

"Kwamitin ya kuma taya shugaba Buhari murna bisa kokarinsa na kawo kudirorin da zasu amfani rayuwar yan Najeriya da dama, kuma ya kaɗa kuri'ar amincewa da gwamnatin."

APC ta yi wa yan Najeriya fatan Alheri

Kazalika sakataren yace APC zata gana da masu ruwa da tsaki da masana harkokin yau da kullum domin tattauna abubuwan da suka shafi yan ƙasa.

Ya kuma bayyana cewa kwamitin CECPC na yi wa yan Najeriya fatan alkairi da kuma fatan zasu sha shagalin kirsimeti lafiya.

A wani labarin kuma Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, Ya faɗi babban matsalar da zata hana zaben 2023

Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi gargaɗin cewa matukar ba'a shawo kan matsalar tsaro ba, babban zaben 2023 ba zai yuwu ba.

Jega yace wajibi a tunkari tsaron kasar nan dagaske, idan kuma ba haka ba babu jam'iyyar da zata amince da zaɓen.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jami'an kwastam sun damke babbar kwantena maƙare da bindigu

Asali: Legit.ng

Online view pixel