Dan majalisar tarayya ya fice daga APC ya koma PDP, Ayu ya faɗi sunan Ministan Buhari dake shirin komawa PDP

Dan majalisar tarayya ya fice daga APC ya koma PDP, Ayu ya faɗi sunan Ministan Buhari dake shirin komawa PDP

  • Wani ɗan majalisar dokokin tarayya daga jihar Benuwai ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP bayan ficewa daga APC
  • Sabon Shugaban PDP, Dakta Ayu, ya bayyana wani ministan Buhari da zai dawo PDP ba da jimawa ba
  • Ɗan majalisa, John Dyeh, yace ya ɗauki matakin komawa PDP ne saboda sabon shugaba kawunsa ne

Benue - Shugaban jam'iyyar PDP, Dakta Iyorchia Ayu, a ranar Litinin, ya yi hasashen cewa ministan ayyuka na musamman, Sanata George Akume, zai fice daga APC ya dawo PDP.

Punch ta rahoto Ayu na cewa Ministan, wanda shine jagoran APC a yankin arewa ta tsakiya, zai sauya sheka zuwa PDP bada jimawa ba.

Ayu ya yi wannan hasashen ne a Gboko, yayin taron karban mamba a majlisar dokokin tarayya, wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Kara karanta wannan

Tabbas jam'iyyar PDP zata sake lashe jihohi akalla 25 a zaben 2023, inji Ayu

Akume da Ortom
Dan majaisar tarayya ya fice daga APC ya koma PDP, Ayu ya faɗi sunan Ministan Buhari dake shirin komawa PDP Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Dailytrust ta rahoto Sabon shugaban PDP yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ɗan ku da ya rasa katabus, George Akume, zai dawo jam'iyyar PDP. Ina faɗin wannan maganar ne bisa iyakacin abinda na sani. A baya na yi hasashen zai ɗaga tsintsiya kuma ta faru.
"Amma yanzun wahayin da aka mun shine zai dawo PDP. Idan ya dawo kada ku ƙi karban shi amma ku tabbatar kun masa wankan tuba, domin inda yake a yanzu, ba ya iya tunani mai kyau."
"Ɗan mu ne wanda ya rasa katabus, wanda ya tafka kuskure. Ku tabbata kun gyara shi kuma ku tabbata tunaninsa ya dawo dai-dai."

Ayu ya karbi ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Gboko/Tarka, John Dyeh, zuwa jam'iyyar PDP, kuma ya yi alƙawarin ba za'a nuna musu banbanci ba.

Meyasa ɗan majalisan ya koma PDP?

Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya yi wa ɗan majisa da sauran masu sauya shekan barka da zuwa jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Dala daya (N409.89) na biya kudin sadaki, Matashin da ya auri yar shekara 70

Shugaban waɗan da suka koma PDP, Honorabul Dyeh, yace ya ɗauki matakin komawa jam'iyyar ne saboda shugabanta na ƙasa kawunsa ne.

A wani labarin na daban kuma mun kawo muku Yadda wani gwamna a Arewa ya kwashi tsabar kudi biliyan N60bn daga lalitar jiharsa

Hukumar EFCC tace sabon sashin da ta kirkiro na fasaha ya fara aiki, domin zuwa yanzun ya gano wasu bayanan sirri.

Hukumar tace ɗaya daga cikin abubuwan da sashin ya bankado shine yadda wani gwamna ya cire kudi daga lalitar jiharsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel