Dala daya (N409.89) na biya kudin sadaki, Matashin da ya auri yar shekara 70

Dala daya (N409.89) na biya kudin sadaki, Matashin da ya auri yar shekara 70

  • Bernard Musyoki ya hadu da masoyiyarsa Jan Spicer a Facebook a shekarar 2017 kuma suka fara soyayya
  • A ranar 29 ga Disamba, 2020, Matar ta yanke shawarar zuwa Afrika domin haduwa da masoyinta
  • Bernard Musyoki ya ce lokacin da ya fadawa mahaifiyarsa zai aureta, sai da tambayeshi shin za ta haihu

Kenya - Bernard Musyoki wani matashin da ya auri Ba-Amurkiya yar shekara 70 yace mutane na sukansa kuma suna zarginsa da cewa kawai yana son zuwa Amurka ne.

A hirar da yayi da jaridar TUKO.co.ke, ya bayyana cewa shi kawai yana sonta ne kuma sadakin akwai rahusa.

Yadda suka hadu

Musyoki, wanda dan jihar Kitui ne a Kenya ya bayyanawa jaridar TUKO.co.ke cewa ya hadu da Deborah ne a manhajar Facebook a shekarar 2017.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar annobar COVID-19

A cewarsa:

"Ni na bukaci mu fara kawance, bayan mako guda, nace mata ta aure ni kuma ta amince."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matashin da ya auri yar shekara 70
Dala daya (N409.89) na biya kudin sadaki, Matashin da ya auri yar shekara 70 Hoto: TUKO.co.ke
Asali: UGC

Kudin sadaki

Yace basu daina tattaunawa da juna ba har karshen Disamban 2020, matar ta yanke shawaran zuwa Kenya domin haduwa da shi.

Yace:

"Muna bacci a dakuna daban-daban kuma mun yi alkawarin ba zamu yi jima'i ba har sai an daura mana aure."
"Maganar sadaki sun ce kawai in kai N409.89 coci matsayin sadaka kuma tace min sadakin kenan."

Yan Najeriya sun yi tsokaci:

Fatima Ta Annabi tace:

"Talauci masifane wannan ai iyace sa'ar kakarshi,Allah yakyauta."

Æthëærmu Prësdœr:

Hhhhhh to wlh Koni yadda nake Shan luguden wahala a Nigeria dana samu wacce zatayi wup Dani wallah Ina fecewa

Zainab Yusuf tace:

Hmmmm... Ba dole yaso taba, ita ba dole tasoshi ba, Abar kaza cikin gashin ta kawai..

Kara karanta wannan

Matana na aure sun guje ni saboda hali na, wani gawurtaccen Barawo ya shiga hannu a Kano

Hauwau Muhammad tace:

Kamar na dankara ashar wallah Wai soyayya nabi soyayya da Dan banzan guda na daushi keyar ta da katako tirrrrr

Salisu Nasiru yace:

Karya yake shege, kudi yabi, tsohuwa saar kakarsa zaice wani yana mugun sonta

Asali: Legit.ng

Online view pixel