Rikicin APC a Zamfara: Tsohon kwamishina ya bar tsagin Yari ya koma na Matawalle

Rikicin APC a Zamfara: Tsohon kwamishina ya bar tsagin Yari ya koma na Matawalle

  • Shahararren dan siyasar jihar Zamfara, Sahabi Liman ya sauya tsagi a jam'iyyar APC ta siyasar Zamfara
  • Sahabi Liman ya kasance tsohon kwamishina a mulkin Yari, wanda kuma a da yake tsagin APC da ke biyayya ga Yari
  • Ya bayyana dalilansa na barin tsagin Yari, inda yace ya gamsu da yadda matawalle yake tafiyar da jam'iyyar

Jihar Zamfara - Alhaji Kabiru Sahabi-Liman ya koma tsagin Gwamna Bello Matawalle na jam’iyyar APC a jihar Zamfara.

Sahabi-Liman, wanda aka nada a matsayin kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki a zamanin mulkin Abdul’aziz Abubakar Yari, ya bayyana matakin ne a ranar Litinin 13 ga watan Disamba.

Rikicin jam'iyyar APC
Rikicin APC a Zamfara: Tsohon kwamishina ya bar tsagin Yari ya koma na Matawalle | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya sanar da hakan ne ta wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na tsagin Matawalle, Yusuf Idris ya fitar, PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kasashen musulman duniya sun yi Allah-wadai da babbaka matafiya a Sokoto

Idris ya ruwaito Sahabi-Liman yana cewa ya shiga tsagin Matawalle ne saboda tsunami na siyasa na saurin cinye sansanin siyasar Yari.

Tsohon kwamishinan ya ce idan aka yi la’akari da yadda lamarin tsohon ubangidan nasa ke ta kara tabarbarewa bai da wata dama da ya wuce ya watsar da shi ya shiga harkar siyasar Matawalle.

Sanarwar ta ce:

“Sahabi-Liman ya kasance dan takarar Sanata a zaben 2019 a karkashin sansanin Yari.
"Tsohon kwamishinan ya bayyana shawararsa na yin watsi da tsohon ubangidansa, a lokacin da ya kai ziyarar nuna goyon baya ga shugaban jam'iyyar APC na jihar, Alhaji Tukur Danfulani a sakateriyar jam'iyyar."

A cewar Idris, tsohon kwamishinan ya yanke shawarar shiga tsagin siyasa na Matawalle ne saboda kokarin da gwamnan yake yi na ci gaban jihar.

Kara karanta wannan

Tsaro: Kungiyar Izala ta yi kira da Buhari ya tashi tsaye, jama’a kuma su dage da addu'a

Ya ce shugaban jam’iyyar APC na jihar, Tukur Danfulani, yayin da ya karbi bakuncin tsohon kwamishinan ya yaba masa bisa yadda ya dauki matakin cikin karfin hali.

Ya ruwaito Danfulani yana cewa APC a karkashin jagorancin Matawalle sun ‘sake suna’ tare da karbar duk ‘yan jam’iyyar ba tare da la’akari da matsayinsu na zamantakewa ba.

Kamar yadda Tribune ta rahoto, rikicin APC dai ya kara kamari tun bayan da aka yi taron gangamin jam'iyyar a jihohi.

Gwamnatin APC ta 'yan koyo ne, mu ne za mu iya gyara Najeriya, inji jam'iyyar PDP

A wani labarin, jam’iyyar PDP a ranar Lahadi ta ce jam’iyyar APC da ke mulkin kasar ta zama kesasashshiya ganin yadda tashe-tashen hankula da zubar da jini da ake yi suka yawaita a fadin Najeriya.

Haka kuma ta ce jam’iyyar APC ta nuna karara cewa ba jam’iyyar siyasa ba ce, taron dangi ne na 'yan koyo, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Samma-kal: Da mulkin farar hular nan, gara gwamnatin Sojoji inji Ministan Obasanjo

Sabon Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologun-Agba, ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai, a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel