Gwamnatin APC ta 'yan koyo ne, mu ne za mu iya gyara Najeriya, inji jam'iyyar PDP

Gwamnatin APC ta 'yan koyo ne, mu ne za mu iya gyara Najeriya, inji jam'iyyar PDP

  • Jam'iyyar PDP ta ta'allaka munanan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da yadda gwamnatin Najeriya ke tafiya
  • Ta ce jam'iyyar APC jam'iyya ce ta 'yan koyo wadanda basu da manufa ko hangen nesa a iya abubuwan da suka bayyana
  • A bangarenta, PDP ta ce ita ce kadai za ta iya dawo da Najeriya kan turba domin ta kware a kan komai da ake bukata

Abuja - Jam’iyyar PDP a ranar Lahadi ta ce jam’iyyar APC da ke mulkin kasar ta zama kesasashshiya ganin yadda tashe-tashen hankula da zubar da jini da ake yi suka yawaita a fadin Najeriya.

Haka kuma ta ce jam’iyyar APC ta nuna karara cewa ba jam’iyyar siyasa ba ce, taron dangi ne na 'yan koyo, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba a sace matafiya a Maiduguri ba: Rundunar soji ta bayyana abin da ya faru

Sabon Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologun-Agba, ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai, a Abuja.

Tutocin jam'iyyar PDP
Gwamnatin APC ta 'yan koyo ne, mu ne za mu iya gyara Najeriya, inji jam'iyyar PDP | Hoto: vanguardngr.com

Ya ce:

“… game da rashin kula ga tashin hankali, rashin kula ga zubar da jini. A duk duniya idan aka samu shugabanci na gaskiya, ba za a tafi hutu a lokacin rikici ba.
"Lokacin da barna ta faru ga kasashe, ana sa ran shugaban kasar zai ci gaba a matsayin babban mai ba da ta'aziyya. Amma a Najeriya, akwai rashin shugabanci kwata-kwata.
“Shi ya sa mutane 40, 50 ke mutuwa a kullum kuma ga alama ba komai. Muna da shugabancin da ya tafi hutu, Najeriya na tarwatsewa a karkashin Janar mai ritaya, abin mamaki."

Da yake bayyana cewa, gwamnatin yanzu ba ta tausayin talaka ko kuma nuna damuwa kan abubuwan da suka shafi talakawa, ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

Bamu taba kwanciyar aure dashi ba, amma 'ya'yanmu hudu, inji tsohuwar matar Fani-Kayode

“Shugaban da bai damu ba. Idan aka kashe mutane maimakon a tausaya musu, sai su zarge su. Ka tuna da manoman da aka kashe a gonakinsu a baya-bayan nan; wani ya ce ba su nemi izinin zuwa gonakinsu ba. Wadanne irin mutane marasa tausayi ne muke da su a matsayin shugabanni?
“Amma na ce ‘yan Najeriya sun fi kowa sani kuma suna son canjawa. Yana da kyau in fadi wani abu karara – APC ba jam’iyya ba ce. Taro ne na dangi kuma 'yan koyo.
“Don haka ne za ku ga cewa duk abin da suke yi ya yi daidai da rudaninsu. Domin su baki ne ’yan uwa masu bambamci, ba ijma’i, ba akida, ba manufa daya, ba hangen nesa iri daya. Don haka da wuya su hada kai. Akwai bambamcin da ba za a daidaita ba a tsakaninsu.”

Ologun-Agba ya ce, a daya bangaren kuma, jam’iyyar PDP ta nuna cewa tana da duk abin da ya dace don dawo da Najeriya kan turba.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Za mu durƙusa har ƙasa don nema wa kudu maso gabas goyon bayan sauran yankuna, Ezeife

PDP dai na wannan martanin ne duba da yadda ake yawan samun hare-hare a yankuna daban-daban na Najeriya, musamman a Arewa.

A makon da ya gabata ne Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton samun afkuwar mummunan lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a jihar Sokoto.

Gwamnati ta yi Allah wadai, amma duk da haka 'yan Najeriya sun bayyana fushinsu kan rashin nuna kulawa daga gwamnati.

'Yan bindiga sun fito da sabon salo a Zamfara, sun saka sabon haraji

A wani labarin, ‘yan bindiga a jihar Zamfara sun fito da sabon salo mai hatsarin gaske yayin da suka bukaci a biya sama da Naira miliyan 1 a matsayin haraji kan yankuna daban-daban a kananan hukumomin Zurmi, Kaura Namoda da Birnin-Magaji na jihar.

Yankunan da abin ya shafa sun hada da Birnin Tsaba, Gabaken Mesa, Gabaken Dan-Maliki, Turawa, Askawa da Yanbuki, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Za mu fatattaki APC daga madafun iko nan da 2023, Jerry Gana

Mazauna wadannan yankuna an ce yanzu haka suna cikin karkashin ‘yan bindigar da suka kafa gwamnatinsu a yankunan da lamarin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel