Da Duminsa: Gwamnan APC ya lashi takwabi, ya ce shi da APC mutu ka raba

Da Duminsa: Gwamnan APC ya lashi takwabi, ya ce shi da APC mutu ka raba

  • Gwamna David Umahi ya mayar da martani kan ikirarin cewa yana shirin komawa jam'iyyar adawa ta PDP
  • Gwamnan na jihar Ebonyi ya karyata wannan ikirarin, yana mai cewa ya gamsu da zaman lafiyar da yake samu a jam’iyyar APC mai mulki
  • Gwamna Umahi ya koka da yadda ‘yan adawa a jihar Ebonyi ke da jin zafi, yana mai cewa ba haka ya kamata ba

Abakiliki, Ebonyi – Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya ce ba shi da wani shiri na komawa jam’iyyar adawa ta PDP.

Mai taimaka wa Gwamna Umahi kan harkokin yada labarai, Francis Nwaze, ya ce gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin godiya ta musamman da aka gudanar a sabon dakin ibada na jihar da ke Abakiliki a ranar Lahadi, 12 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Ba dalilin da zai sa APC ta sha ƙasa a zaben 2023 domin yan Najeriya na jin dadin mulkin Buhari, Gwamna

Gwamnan Ebonyi, Umahi
Da Duminsa: Gwamnan APC ya lashi takwabi, ya ce shi da APC mutu ka raba | Hoto: vanguardngr.con
Asali: Facebook

Legit.ng ta lura cewa an yi ta rade-radin cewa gwamnan da ya koma APC a watan Nuwamba na 2020 na iya tunanin komawa jam'iyyar PDP.

Sai dai Nwaze ya ce Gwamna Umahi ya yi watsi da rade-radin cewa yana shirin komawa PDP, yana mai cewa ya gamsu da zaman lafiyar da ke cikin jam’iyyar APC mai mulki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An jiyo gwamnan na jihar Ebonyi yana cewa:

“Sun ce ina so in koma PDP, tare da wadannan nasarorin?, mutumin da ko hanyar gidansa ba shi da shi, na ce Allah kada ya gafarta masa.
"Na ce na gode wa 'yan adawa a jihar Ebonyi, adawa a jihar Ebonyi na da daci, ba haka ya kamata ba."

Jigon APC ya bayyana sirri, ya zayyano yadda Atiku ya nemi sadakan kudi daga Tinubu

A wani labarin, kamar yadda Cif Bisi Akande, tsohon shugaban APC, ya yi ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya nemi kudi daga hannun Bola Tinubu, shugaban APC na yanzu a lokacin da ya dauki fito takara a shekarar 2007.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Wata na 8 ina neman Ganduje ido rufe domin sasanci, Shekarau

Ya bayyana hakan ne a cikin littafin tarihin rayuwarsa mai suna “My Participations” wanda aka kaddamar a Legas ranar Alhamis, inji rahoton Daily Trust.

A yakin neman zabe da Obasanjo a shekarar 2007, Atiku ya fice daga PDP inda ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar AC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel