Rikicin APC a Kano: Wata na 8 ina neman Ganduje ido rufe domin sasanci, Shekarau

Rikicin APC a Kano: Wata na 8 ina neman Ganduje ido rufe domin sasanci, Shekarau

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya yi karin bayani dangane da rikicin cikin jam’iyyar APC
  • Ya bayyana yadda ya kwashe watanni takwas yana son ganin gwamna Abdullahi Ganduje amma abin ya ci tura
  • Ya bayyana hakan ne a wata tattauna da menena labarai su ka yi da shi inda yake cewa ya yi kokarin kiyaye matsala amma gadarar Ganduje ta ki bari

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya yi bayani dalla-dalla akan rikicin cikin jam’iyyar APC inda ya bayyana yadda ya kai watanni 8 yana son haduwa da gwamna Abdullahi Ganduje amma abin ya ci tura, Tribune Online ta ruwaito.

“Kun gani, tun watan Maris na 2021 rabon da in hadu dashi. Idan zan kirga yanzu mun kai watanni 8 ina kokarin haduwa da shi amma ya ki bani dama,” a cewar Shekarau.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Da alamu Tinubu zai koma tsagin Shekarau, sun yi ganawar sirri

Rikicin APC a Kano: Wata na takwas ina neman Ganduje ido rufe, Shekarau
Rikicin APC a Kano: Wata na takwas ina neman Ganduje ido rufe, Shekarau. Hoto daga tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Yayin tattaunawa a wata hira da suka yi da VOA, Sanata Shekarau ya ce ya dade yana son daidaitawa amma gadarar gwamnan ta ki bari.

Tribune Online ta ruwaito cewa, a cewar Shekarau, hadimin gwamnan da ya nema akan ganin gwamnan ya san abinda yake fadi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A matsayina na tsohon gwamna kuma sanata mai ci, ina tunanin na cancanci a girmama ni. Ko Ganduje ba zai girmama ni da kyau ba, ai ko yaya dai ya kamata ya duba.
“A wannan halin muka tsinci kawunanmu. A matsayina na sanata bansan komai da ke faruwa ba. Gwamna ne yake yin yadda yaso ba tare da tuntubar manyansa da ‘yan jam’iyyarsa ba.
“Manyan ‘yan jam’iyya mun kai 20 a jihar Kano wadanda ya mayar gefe guda. A cikinmu akwai Musa Gwadabe, mai shekaru 80, ministan tsaro (Magashi), Janar Jaafaru Isa da sauransu.”

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kwankwaso ya yi magana kan rikicin Ganduje da Shekarau a APC jihar Kano

Shekarau, wanda yanzu haka Sardaunan Kano ne, ya kula da yadda komawar Ganduje gefe guda ya zama babbar matsala.

Ya kara da cewa:

“Shugaban jam’iyyar wanda yariman masarautar Kano ne ya ce a Kano APC ta Ganduje ce, matarsa da masarautar. Kuma duk wanda hakan bai yi masa ba ya bar jam’iyyar.”
Shekarau ya bayyana cewa "bayan duba komai, kuma muka ga ko taron jam’iyya za a yi ba a samu, nan muka fahimci ba a bukatarmu a jam’iyyar.
“Har bayan wani taro da muka yi daban, mun fahimci so suke yi mu dinga yin shiru suna cin karensu babu babbaka, sai muka maka su a kotu,” a cewar Shekarau.

Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin ta na garkame ofishin lauyan Shekarau

A wani labari na daban, Gwamnatin jihar Kano ta yi karin haske kan dalilin da yasa ta garkame ginin ofishin Barista Nuraini Jimoh.

Daily Trust ta ruwaito yadda Jimoh, daya daga cikin lauyoyin Malam Ibrahim Shekarau da wasu ma'aikatansa aka garkamesu na tsayin sa'o'i a cikin ofishinsa bayan umarnin gwamnatin.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi magana kan daliban Islamiyya 20 da suka mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kano

Lamarin ya auku ne bayan sa'o'i 24 da tsagin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na Shekarau ya lallasa Gwamna Abdullahi Ganduje a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel