2023: Buhari Ya Yi Hasashen Manyan Abubuwa Da Za Su Faru Zaben Shugaban Ƙasa Na Gaba

2023: Buhari Ya Yi Hasashen Manyan Abubuwa Da Za Su Faru Zaben Shugaban Ƙasa Na Gaba

  • Ana ta hasashe akan abinda zai iya faruwa don zama mafita ga ‘yan Najeriya dangane da zaben shugaban kasa mai zuwa na shekarar 2023
  • Wannan karon kuwa da kan shi shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yi hasashen inda ya ce za a yi zabe cikin nasara da zaman lafiya
  • Shugaban kasan ya yi wannan tsokacin ne a ranar Juma’a, 10 ga watan Disamba, a wani taro na yanar gizo da su ka yi inda ya ce zai mika mulki cikin lumana

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi hasashe dangane da zaben shugaban kasa na 2023, inda ya ce za a yi zaben gaskiya da gaskiya ne kuma cikin nasara.

Shugaban kasan ya yi hasashe akan cewa bayan sabon shugaban kasan da za a zaba, akwai mika mulki cikin lumana da zai auku, Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba zata saɓu ba, Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan Kwamishina a jihar Katsina

2023: Buhari Ya Yi Hasashen Manyan Abubuwa Da Za Su Faru Zaben Shugaban Ƙasa Na Gaba
Za a yi adalci a babban zaben 2023, a mika mulki ba tare da matsala ba, Buhari. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Shugaba Buhari ya yi wannan tsokacin ne wanda ya zama kamar alkawari a ranar Juma’a, 10 ga watan Disamba yayin wani taro da su ka yi ta yanar gizo na kasa da kasa wanda shugaba Joe Biden na Amurka ya shirya, Daily Nigerian ta kara.

A cewar Buhari, gwamnatin tarayya ta na iyakar kokarin ganin ta jajirce don tabbatar da an yi zabe mai inganci a zabe mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kasan ya ce kasar nan za ta ci gaba da bunkasa dimokradiyya a Afirka ta yamma da ma nahiyar baki daya duk da bakin junyin mulkin da ya auku a wasu kasashen.

Kamar yadda ya ce:

“Yayin da mu ke dosar zaben 2023, za mu ci gaba da dagewa wurin yin duk wasu abubuwan da su ka dace don tabbatar da cewa ba mulki cikin luman kadai aka mika ba, har da tabbatar da an yi zaben gaskiya da gaskiya.

Kara karanta wannan

Ana yi wa Shugaban kasa martani a kan zuwa Legas, ana makokin mutum 80 a Sokoto

“Ran ku ya dade, Najeriya ta na ci gaba da bin bayan dimokradiyya a yammacin nahiyar Afirka da ma Afirka gaba daya. Amma abun ban takaicin shi ne yadda dimokradiyyar da aka gina tsawon shekaru ta ke fuskantar kalubalen juyin mulki.”

Karanta cikakken jawabin Buhari a wallafar da Femi Adesina ya yi a Facebook:

Ganduje Vs Shekarau: Kotun ɗaukaka ƙara ta tsayar da ranar sauraron shari'ar zaɓukan shugabannin APC na Kano

A wani labarin, kotun daukaka kara ta sa rabar 16 ga watan Disamban 2021 ta zama ranar sauraron kara don sanin matsaya daga hukunci da babbar kotun FCT wacce ta wofantar da gangamin gundumar Kano na APC a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Hedkwatar jam’iyyar ta kasa ta ce mambobin kwamitin shirya gangami ne su ka daukaka karar gaban kotun da ke Abuja a ranar Litinin.

A wata takarda wacce kwamishinan labarai na Kano, Malam Muhammad Garba ya saki a ranar Talata, ya ce APC tana jiran jin hukuncin kotun don sanin matakin gaba.

Kara karanta wannan

Buhari: Dalilan da suka sa rashin tsaro ba zai hana masu zuba hannayen jari zuwa Najeriya ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel